Dollar

38,0482

0.02 %

Euro

43,2660

0.07 %

Gram Gold

3.945,1200

0.47 %

Quarter Gold

6.469,8500

0 %

Silver

39,5100

-0.19 %

Hasashe ya nuna cewa magidanta miliyan 23.3 daga cikin miliyan 52.6 za su kasance su kaɗai ba tare da abokan ba zuwa 2050.

Kimanin gawawwaki 42,000 ne ba a karbe su ba a Japan a 2023, a cewar wani rahoto

Kusan gawawwaki 42,000 ba a karɓe su ba a Japan a ashekarar 2023, a yayin da yawan tsofaffi da ke rayuwa su kaɗai ya ƙaru, a cewar wani rahoton gwamnati.

Hukumomin yankin suna ƙone gawawwakin ko kuma a binne su, a cewar wani bincike irinsa na farko, kamar yadda kafar watsa labarai ta Tokyo, Kyodo News ta rawaito a ranar Lahadi.

Gwawakkin 41,969 da aka iya gane su da na waɗanda ba a iya gane su ba, sun kai kaso 2.7 cikin ɗari na mutanen da suka mutu a 2023.

Binciken, wanda Ma’aikatar Lafiya da Ayyuka da Walwalar Jama’a ta ƙaddamar, ya nuna cewa mafi yawancin ƙananan hukumomi ba su da tsari mai kyau na yadda za a kula da gawawwaki, ciki har da tsawon lokacin da za a bar su kafin a ƙona su.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake nuna damuwa cewa iyalai za su iya neman karɓar gawawwakin bayan an ƙone su.

Dokar makabartu da binne mamata da sauran ƙa'idoji ta tanadi cewa idan ba a samu wanda zai karɓi gawa ba, to hukumomin ƙaramar hukuma a inda aka yi mutuwar su ƙona gawar.

Binciken kan yadda ƙananan hukumomi a duk faɗin ƙasar ke kula da gawawwakin da ba a nemi a karɓe su ba, wanda shi ne irinsa na farko, ya gano cewa kashi 11.3 cikin ɗari na ƙananan hukumomi ne kawai ke da tsarin yadda za a yi da gawawwakin da ba a nemi a karɓe su ba.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#