Dollar

38,1137

0.18 %

Euro

42,0543

-0.85 %

Gram Gold

3.708,4600

-2.33 %

Quarter Gold

6.293,2300

-0.18 %

Silver

36,1600

-6.93 %

Ƙasashen yankin Sahel, waɗanda suka kori sojojin ƙasashen Yammacin duniya daga cikinsu, yanzu haka suna ƙarfafa alaƙa da Moscow domin samun tallafi kan harkokin tsaro.

Rasha ta sha alwashin taimaka wa ƙasashen Burkina Faso, Mali da Nijar a fannin soji

Rasha ta tattauna da ƙasashen yankin Sahel kan yadda za su bunƙasa alaƙar soji, inda ta yi alƙawarin bayar da horo da samar da makamai a yayin da take ƙarfafa dangantaka tsakaninta da ƙasashen da ke Yammacin Afirka bayan sun kori dakarun Faransa.

Ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov ne ya bayyana haka ranar Alhamis bayan ya gana da takwarorinsa na ƙasashen Mali, Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar a birnin Moscow, yana mai cewa a shirye suke su taimaka domin bunƙasa alaƙar soji da ƙasashen.

“Ina jaddada aniyar Moscow ta taimakawa domin samar da gamayyar rundunar soji ta yankin Sahel, tare da ƙarfafa dakarun soji da sauran jami’an tsaro na waɗannan ƙasashe uku ta hanyar ba su horo da makamai,” in ji Lavrov.

Babban jami’in diflomasiyyar na ƙasar Rasha ya zargi Ukraine da ta’azzara rashin tsaro a yankin, yana mai cewa tana "goyon bayan ƙungiyoyin ‘yan ta’adda a fili ƙarara a wannan ɓangare na Afirka yayin da masu ɗaure mata gindi na ƙasashen Yamma suka zura mata ido," ko da yake bai bayar da wata hujja ta wannan zargi ba.

Ministan harkokin wajen Mali Abdoulaye Diop ya jaddada zargin da Lavrov ya yi wa, yana mai cewa ƙasarsa tana kallon Ukraine a matsayin “ƙasar ta’addanci.”

"Muna da ra’ayi iri ɗaya game da yaƙi da rashin tsaro da ta’addanci a yankinmu, waɗanda wasu ƙasashen waje da ‘yan-korensu da ke yankin suke ingizawa," in ji shi.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#