Dollar
35,4431
0.27 %Euro
36,3540
-0.47 %Gram Gold
3.063,1500
1.01 %Quarter Gold
4.997,4300
-0.04 %Silver
34,5800
1.03 %Rundunar 'yan sandan Nijeriya reshen Jihar Kebbi ta tabbatar da lamarin inda ta ce wasu 'yan ta'adda waɗanda ake zargin Lakurawa ne sun kashe ma'aikatan na Airtel uku da kuma wani mutumin ƙauyen Gumki a Ƙaramar Hukumar Arewa ta Jihar Kebbi.
Wasu ‘yan bindiga waɗanda ake zargin mambobi ne a ƙungiyar ta’addanci ta Lakurawa sun kashe ma’aikatan kamfanin sadarwa na Airtel uku da kuma wani mutum guda wanda ya fito daga ƙauyen Gumki a Ƙaramar Hukumar Arewa ta Jihar Kebbi.
Mai magana da yawun ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Kebbi CSP Nafiu Abubakar ne ya tabbatar da lamarin a wata sanarwa da ya fitar.
“A ranar 10/01/2025 da misalin 8:47 na dare, wasu da ake zargin Lakurawa ne sun kai hari wani wuri da ake ginawa a ƙauyen Gumki da ke Ƙaramar Hukumar Arewa, wanda ke kan iyakar Nijeriya da Nijar inda ma’aikatan Airtel ke haɗa wasu na’urorin tsaro ga Hukumar Kula da Shige da Fice ta Nijeriya,” in ji shi.
“Sakamakon haka, mutum huɗu sun rasu, ɗan garin mutum ɗaya sai ma’aikatan Airtel uku.”
“Bayan samun rahoton lamarin, sai kwamishinan ‘yan sanda na Kebbi CP Bello M Sani tare da Kwanturola na hukumar Immigration reshen Kebbi CIS Muhammad Bashir Lawali suka garzaya wurin da lamarin ya faru inda aka kwashe gawawwakin zuwa asibitin Sir Yahaya Memorial Hospital, Birnin Kebbi.”
Mai magana da yawun ‘yan sandan ya tabbatar da cewa tuni kwamishinan ‘yan sandan jihar ya bayar da umarnin zaƙulo Lakurawan da ake zargi domin yaba wa aya zaƙinta.
A ƙarshen shekarar 2024 ne ƙungiyar Lakurawa ta yi ƙaurin suna a Nijeriya inda har rundunar sojin ƙasar ta ayyana ta a matsayin ƙungiyar ta’addanci.
A kwanakin baya jami’an tsaron ƙasar sun bayyana cewa suna aikin fatattakar ‘yan ta’addan na Lakurawa.
Comment