Dollar

35,4431

0.27 %

Euro

36,3540

-0.47 %

Gram Gold

3.063,1500

1.01 %

Quarter Gold

4.997,4300

-0.04 %

Silver

34,5800

1.03 %

Continents

Categories

Ziyarar ta shugaban Somalia Hassan Sheikh Mohamud  na zuwa ne bayan sulhun da ƙasashen biyu suka yi wanda Turkiyya ta jagoranta a Ankara.

Shugaban Somalia ya kai ziyara Ethiopia a karon farko bayan Turkiyya ta sulhunta ƙasashen biyu

Shugaban ƙasar Somalia Hassan Sheikh Mohamud ya isa Ethiopia ranar Asabar a karon farko tun bayan da ƙasashen biyu suka yi sulhu wanda Turkiyya ta jagoranta.

Firaministan Ethiopia Abiy Ahmed ya yi wa Mohamud kyakkyawar tarba, sannan shugabannin biyu sun tattauna kan yadda za su kyautata alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu, kamar yadda Abiy Ahmed ya bayyana a saƙon da ya wallafa a shafinsa na X.

"Wannan ziyara na zuwa ne bayan yarjejeniyar da aka ƙulla a kwanakin baya wacce Ankara ta jagoranta. Wannan haɗin-kai wani sabon babi ne na dangantaka tsakanin Somalia da Ethiopia,” a cewar wata sanarwa da Fadar shugaban ƙasar Somalia ta fitar.

Turkiyya ta jagoranci ‘sasantawa mai tarihi’ tsakanin Somalia da Ethiopia

Rikici ya ɓarke tsakanin Ethiopia da Somalia a watan Janairun 2024, bayan Ethiopia ta ƙulla yarjejeniya da yankin Somalilanda wanda ya ɓalle daga Somalia kan amfani da tashar jiragen ruwa ta Berbera domin isa Bahar Maliya.

Tun daga wancan lokacin, Turkiyya ta riƙa kai mari tana kai gwauro domin ganin ta sulhunta ƙasashen biyu.

A watan Disamba ne ƙasashen biyu suka sulhunta a Ankara lokacin da shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya karɓi baƙuncin shugaban Somalia da firaministan Ethiopia.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet