Dollar

35,4431

0.27 %

Euro

36,3540

-0.47 %

Gram Gold

3.063,1500

1.01 %

Quarter Gold

4.997,4300

-0.04 %

Silver

34,5800

1.03 %

Continents

Categories

Kwamandan Rundunar RSF ta Sudan Hamdan Daglo ya tabbatar da cewa sun rasa iko da birnin Wad Madani wanda shi ne babban birnin Jihar Al-Jazira ta Sudan.

Sojojin Sudan sun sake ƙwace wani muhimmin birni daga hannun dakarun RSF

Kwamandan rundunar RSF ta Sudan ya ce dakarunsa sun rasa iko da “Wad Madani”, wanda shi ne babban birnin Jihar Al-Jazira a ranar Asabar a lokacin da sojojin ƙasar sunka ƙaddamar da wani farmaki.

A wani saƙon murya da ya aika ga mayaƙansa da kuma jama’ar Sudan, Mohamed Hamdan Daglo ya sha alwashin “ƙwace iko da duk” wasu biranen tsakiyar Sudan, waɗanda ke ƙarƙashin ikon RSF tun daga Disambar 2023.

Sojojin waɗanda ke yaƙi da RSF tun daga Afrilun 2023 sun bayyana cewa sun shiga birnin ne a ranar Asabar domin kawar da “ɓurɓushin ‘yan tawaye.”

Jami’an gwamnati waɗanda ke biyayya ga sojojin ƙasar sun yi jinjina dangane da sake ƙwace iko da muhimmin birnin wanda ya kasance ya haɗa jihohi da yawa.

Haka kuma shi ne birni mafi kusa da Khartoum babban birnin Sudan da yaƙi ya ɗaiɗaita inda yake da nisan kilomita 200 daga birnin.

Tun bayan fara yakin, ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba mutum miliyan 12 da muhallansu, kusan miliyan tara daga cikinsu sun kasance a cikin kasar, a wani lamari da Majalisar Dinkin Duniya ta ce shi ne rikicin gudun hijira mafi girma a duniya.

A farkon watannin yakin, kusan mutane rabin miliyan ne suka nemi matsuguni a Al-Jazira, kafin wani hari da RSF ta kai ya ra ba fiye da mutum 300,000 da muhallansu a watan Disamba 2023, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet