Sport
Dollar
38,1561
0.06 %Euro
43,6774
-0.13 %Gram Gold
4.081,7800
-0.41 %Quarter Gold
6.731,9300
0 %Silver
39,8600
-0.81 %‘A karon farko, Iraki da Turkiyya na kaddamar da wani shiri na dogon zango da ya zarta batun kasuwanci,’ in ji Shugaban Asusun Ci-gaban Iraki a loakcin da bangarorin biyu ke sanya hannu kan yarjejeniyar zurfafa alakarsu.
Asusun Arzikin Turkiyya (TVF) da Asusun Ci-gaban Iraki (DFI) sun sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna a Bagadaza don assasa haɗin kai da ke da manufar haɓaka ayyukan haɗin gwiwa a muhimman ɓangarori.
Shugaban TVF kuma mamban hukumar, Salim Arda Ermut da Daraktan Zartarwa na DFI Mohammed al Najjar ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar.
A wajen taron ‘yan jaridu da aka gudanar kafin sanya hannun, Ermut ya yi karin haske kan alaƙar tarihi da raya al’adu tsakanin ƙasashen biyu.
Ya ce “A yayin da ƙasashen da ke da daɗaɗɗen tarihi suke a yanki guda da tsatso daya, Turkiyya da Iraƙi sun jima suna amfana da dangantakarsu ta musamman,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa alaƙar da ɗaruruwan shekaru ta girmama juna zuwa hadin kan da aka gina kan aminci da juna da manufofin bai daya.
Ƙudirce niyyar aiki tare a muhimman ɓangarori
Da yake bayyana yarjejeniyar a matsayin babban matakin matsa wa gaba, Ermut ya ce yarjejeniyar za ta ƙarfafa haɗin kai tsakanin Turkiyya da Iraki ba a matakin yanki kawai ba, har da a fagen kasa da kasa.
“A matsayin Asusun Arzikin Turkiyya, za mu haɗa kai da Asusun Ci-gaban Iraƙi don haɓakawa, da ɗaukar nauyi da aiwatar da ayyuka da dama,” in ji shi.
“Yarjejeniyar na bayyana niyyarmu ta aiki tare a muhimman ɓangarori ƙarara.” in ji shi. “Haɗin kanmu zai shafi ɓangarorin makamashi mai sabuntuwa, da fasahar sadarwa da ƙere-ƙere, da gina ƙasa da samar da kayan more rayuwa, da sufuri da dakon kayayyaki, da ababan hawa, da ci-gaban noma da samar da abinci, tare da ayyukan kudi da kamfanoninin aika kuɗaɗe.”
Ermut ya kuma ƙara da cewa haɗin kan zai kuma wuce zuba jari kawai, inda zai haɗa da musayar ilimi, da fasahar ƙere-ƙere da haɗin gwiwar amfani da arzikin juna.
'A karon farko Turkiyya da Iraki na kaddamar da muhimmin shiri mai manufar cim-ma wa a dogon zango da ta haura batun kasuwanci’
Al Najjar ya marabci wakilan TVF a Bagadaza inda ya ce ziyararsu ta zama wata babbar gaɓa - ba ga Ci-gaban Hanya Kawai ba, har ma ga faffaɗen haɗin kai.
“A karon farko, Iraki da Turkiyya na daukar matakin da ya wuce na kasuwanci inda suke ƙulla shiri a fannoni masu muhimmanci da za a cim-ma a dogon zango,” in ji shi, yana mai ƙara wa da cewar yarjejeniyar ta shimfiɗa tushe ga haɗin gwiwa a nan gaba.
Me ya yarjejeniyar ta kunsa?
Yarjejeniyar ta assasa mataki mai zurfi na haɗin kai da manufar gina haɗin gwiwa mai tasirin gaske a matakin yanki da fagen ƙasa da aƙsa. Ta assasa yanayi da tsarin hadin gwiwa wajen aiwatar da ayyuka, inda a watan Mayun 2025 za a fara ganin sakamako a zahiri.
Yarjejeniyar ta kuma haɗa da samar da zuba jari a fannoni masu muhimmanci kamar makamashi da ake iya sabuntuwa, da fasahar sadarwa da ƙere-ƙere, da gina ƙasa da samar da kayan more rayuwa, da sufuri da dakon kayayyaki, da ababan hawa da ci-gaban noma da samar da abinci, tare da ayyukan kudi da kamfanoninin aika kudade.
Baya ga zuba jari, yarjejeniyar ta kuma jaddada samar da hadin kai a fannin musayar ilimi, fasahar kere-kere da amfani da arzikin juna.
Ana sa ran hadin kan zai taimaka wajen samun ci-gaban tattalin arziki mai dore wa a tsakanin Turkiyya da Iraki, da habaka karfin tattalin arzikin yankin, da karfafa dadaddiyar dangakantakar kasashen biyu.
Comments
No comments Yet
Comment