Sport
Dollar
38,1214
0.1 %Euro
43,6183
1.34 %Gram Gold
4.045,1500
2.27 %Quarter Gold
6.511,6500
0 %Silver
40,2600
1.68 %Erdogan ya ce Turkiyya za ta ci gaba da kokarin diflomasiyya don neman ɗage takunkuman duniya da aka saka wa Siriya, kuma dole ne a ƙara kokarin haɓaka hadakar tattalin arziki da ta cinikayya tsakanin kasashen biyu.
Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya gudanar da wata muhimmiyar ganawa da Shugaban Siriya, Ahmed al Sharaa, a yayin Taron Diflomasiyya na Antalya karo na huɗu, wanda ke nuna yiwuwar farfaɗo da dangantaka da kuma mayar da hankali kan zaman lafiya a yankin.
A cewar wata sanarwa da Hukumar Sadarwa ta Türkiye ta fitar a ranar Juma’a, shugabannin biyu sun tattauna kan dangantakar ƙasashen biyu, tare da duba batutuwan yankin da na duniya gaba ɗaya.
Wannan ganawa ta zama wata muhimmiyar alama ta diflomasiyya, musamman bayan shekaru na rashin jituwa tsakanin Ankara da Damascus.
Goyon baya ga zaman lafiya da cikakken iko
Shugaba Erdogan ya bayyana jin daɗinsa na cewa an samu nasarar daƙile ƙoƙarin tayar da tarzoma a Siriya, tare da nuna fata mai kyau game da makomar ƙasar.
“Shekaru masu zuwa za su kasance na zaman lafiya da wadata da kwanciyar hankali ga Siriya,” in ji Erdogan, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Ya kuma jaddada daɗaɗɗen matsayin Turkiyya na goyon bayan cikakken ikon Siriya da yankunanta, tare da jaddada cewa Ankara za ta ci gaba da bayar da gudunmawa wajen samar da tsarin zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Ƙarfafa haɗin gwiwar tattalin arziki da sassauta takunkumi Shugaban Turkiyya ya jaddada muhimmancin ƙarfafa dangantakar kasuwanci da tattalin arziki da Siriya, tare da kira ga farfaɗo da haɗin gwiwa a waɗannan fannoni.
Ya bayyana cewa Türkiye za ta ci gaba da ƙoƙarin diflomasiyya don ganin an ɗage takunkuman ƙasa da ƙasa da aka ƙaƙaba wa Siriya, waɗanda suka hana farfaɗowar tattalin arziki da haɗin kai a yankin.
Haka kuma, an ruwaito cewa ɓangarorin biyu suna tattauna yiwuwar ɗaukar matakai na gaba a wasu fannoni na haɗin gwiwa, wanda ya nuna aniyar da ke akwai na farfaɗo da dangantaka ta hanyar moriyar juna.
Sauyin yanayin diflomasiyya Wannan ganawa ta zo ne a daidai lokacin da ake samun sauyi a yanayin diflomasiyyar yankin. A cikin shekarun baya-bayan nan, wasu ƙasashen Larabawa sun fara sake tattaunawa da gwamnatin Siriya bayan kifewar gwamnatin Bashar al Assad, wanda ya biyo bayan fiye da shekaru goma na ware ta da aka yi a fannin diflomasiyya tun bayan yaƙin basasar 2011.
Sake farfaɗo da dangantaka da gwamnatin Siriya na iya yin tasiri mai girma kan diflomasiyyar yankin da tsaro da kuma kula da batutuwan ƙaura.
Taron Diflomasiyyar na Antalya, wanda yanzu ya kai karo na huɗu, ya zama wani muhimmin dandalin tattaunawa na ƙasa da ƙasa, inda shugabannin ƙasashe da jakadun da masana da shugabannin al’umma ke haɗuwa don tattauna ƙalubalen duniya ta hanyar diflomasiyya.
Comments
No comments Yet
Comment