Dollar

38,2552

0.34 %

Euro

43,8333

0.15 %

Gram Gold

4.076,2000

0.31 %

Quarter Gold

6.772,5700

0.78 %

Silver

39,9100

0.36 %

Hukumar EFCC ta tabbatar da cewa za ta haɗa kai da hukumar ‘yan sanda ta ƙasa da ƙasa Interpol domin bin diddigin waɗanda ke da hannu wajen wannan babbar damfara a cikin gida da waje.

EFCC za ta haɗa kai da Interpol don bincike kan damfarar  hannayen-jarin CBEX

Hukumar Yaki da Yi wa Tattalin Arzikin Kasa zagon Kasa a Nijeriya (EFCC) ta ƙaddamar da wani gagarumin bincike kan zargin damfarar Naira Tiriliyan 1.3 da ake alaƙantawa da tsarin saka hannun-jari na intanet na kamfanin CryptoBank Exchange (CBEX).

 Hukumar EFCC ta tabbatar da cewa za ta haɗa kai da hukumar ‘yan sanda ta ƙasa da ƙasa Interpol domin bin diddigin waɗanda ke da hannu wajen aikata wannan laifin a cikin gida da waje.

 Kamfanin na CBEX, wanda rahotanni ke cewa wasu ‘yan ƙasashen waje ne tare da haɗin gwiwar ‘yan Nijeriya ne ke gudanar da shi, ya ruguje a ranar Litinin, lamarin da ya rufe wa dubban mutane da suka zuba jari a kamfanin asusunsu.

 Mutane da dama sun wayi gari babu ko sisi a cikin asusan jarinsu, inda dandalin ya nemi a saka wasu ƙarin  kuɗaɗe kafin mutum ya samu damar dawo da asusunsa.

Duk da cewa har yanzu ba a kai ga tantance takamaimai girman asarar da aka yi a hukumance ba, wasu rahotannin da ba a tabbatar ba sun ƙiyasta kuɗaɗen da aka sace sun haura dala miliyan 847 kwatankwacin Naira tiriliyan 1.3, lamarin da ya shafi masu zuba jari daga Nijeriya da na ƙasashen waje.

CBEX, wanda ya yi alƙawarin samar da ribar kashi 100 cikin 100 a cikin kwanaki 30 ta hanyar kasuwancin intanet, daga ranar 9 ga watan Afrilun 2025 ya fara nuna alamun rugujewa.  

Tuni dai EFCC ta fara gudanar da bincike kafin rugujewar kamfanin bayan bayanan sirri da aka samu, a cewar mai magana da yawun hukumar ta EFCC, Dele Oyewale

“Muna da bayananmu kafin faruwar lamarin, mun riga mun soma bincike a kai, amma yanzu da hannun jarin ya ruguje, za a saka waɗanda ke da ruwa da tsaki a ciki,” kamar yadda ya shaida wa manema a ranar Talata.

Kazalika ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa hukumar EFCC ta duƙufa wajen fallasa tare da wargaza duk wani shirin damfara kamar CBEX.

“Akwai ire-iren wannan shiri na damfara a faɗin ƙasar nan, waɗanda mutane ba su san da su ba, kuma muna ƙoƙarin gano su, muna haɗa kai a cikin gida, yayin da a ɓangare guda muke haɗa kai da Interpol domin zaƙulo masu aikata wanan laifi a ƙasashen waje,” in ji Oyewale.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#