Dollar

38,1325

0.13 %

Euro

43,5508

1.16 %

Gram Gold

4.060,6400

2.66 %

Quarter Gold

6.716,2100

3.14 %

Silver

40,5300

2.35 %

Nijeriya, duk da arzikin manta, tana yawan fuskantar ƙarancin mai da dogayen layukan ababen hawa da ke neman mai.

Nijeriya za ta aiwatar da gagarumin shirin adana man fetur domin kauce wa ƙarancinsa

Nijeriya na shirin samar da wata matattarar adana fetur a wannan shekarar domin tsare tattalin arzikin ƙasar daga samun tangarɗa a kasuwar duniya, kamar yadda hukumar da ke sa ido kan harkokin man ƙasar ta bayyana a wani taron manema labarai ranar Talata.

Farouk Ahmed, shugaban hukumar da ke kula da jigilar ɗanyen mai da tace mai ta Nijeriya, ya ce ajiyar, wadda dokar man ƙasar ta ba da ikon yi, za ta rage raɗaɗin rashin mai da kuma ƙara dogaro da kai a fannin makamashi.

Nijeriya, duk da da arzikin manta, tana yawan fuskantar ƙarancin mai da kuma dogayen layukan sayen mai.

Ƙasar tana son ta haɓaka ƙarfinta na iya tace mai a cikin gida, musamman matatar man Dangote mai iya tace gangar ɗanyen mai 650,000 a yini, wajen inganta juriyar tattalin arzikinta ga tangardar da za a iya samu a kasuwar duniya.

Ajiya don tsaro

Yayin da Nijeriya a halin yanzu take da mai da za ta iya amfani da shi na kwanaki 30, Ahmed ya ce sabon shirin ajiya na musamman wanda aka shirya bisa irin shirin ajiyar mai na Amurka, zai faɗaɗa sosai.

Sai dai kuma bai bayyana iya yawan man da za a ajiye ba.

Dokar fannin man Nijeriya ta bai wa hukumar damar ba da lasisin ajiyar mai da yawa ga wuraren ajiyar mai masu zaman kansu su iya adana mai har zuwa lokacin da ake so.

Fara aikin matatar man Dangote a watan Satumba, tare da wasu ƙananan matatun mai biyar, ya rage yawan man da Nijeriya ke shigarwa ƙasar matuƙa daga lita miliyan 50.8  a yini a watan Satumba zuwa lita miliyan 28.7 a yini a watan da ya gabata.

Kawar da shigar da mai

Alƙaluma daga hukumar da ke sa ido a fannin sun nuna cewa matatun mai da ke aiki a cikin ƙasar za su iya tace gangar mai 770,500 a yini zuwa watan Yuni.

Hukumar ta bayyana kyayyawan fatanta cewa faɗaɗa yawan man da ake tacewa a ƙasar zai iya kawo ƙarshen shigar da tataccen mai ƙasar.

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#