Sport
Dollar
38,2050
0.27 %Euro
44,0838
1.33 %Gram Gold
1.167,0000
-1.35 %Quarter Gold
6.947,4100
2.66 %Silver
40,3100
0.99 %Ya rasu a ranar Litnin da misalin ƙarfe 7:35 na safe (0535 GMT) bayan ya yi fama da “sanyin haƙarƙari”.
Fafaroma Francis ya rasu yana da shekara 88 bayan ya sha fama da rashin lafiya, kamar yadda Fadar Vatican ta sanar a ranar Litinin.
Ya rasu a ranar Litnin da misalin ƙarfe 7:35 na safe (0535 GMT) kamar yadda Fadar Vatican ta sanar.
Ya yi fama da “sanyin haƙarƙari” tare kuma da ciwon thrombocytopenia, kamar yadda sanarwar Vatican ɗin ta baya ta tabbatar.
An haifi Francis a Buenos Aires a ranar 17 ga Disambar 1936, iyayensa ‘yan ci rani ne daga ƙasar Italiya.
Ya yi karatu a Argentina inda daga baya ya tafi Jamus kafin daga baya a shekarar 1969 ya samu matsayin limamin majami’a na Cocin Katolika.
Tsawon shekarun da ya shafe a matsayinsa na fafaroma, Francis ya kasance mutumin da ake ƙauna kuma wanda ya rinƙa jawo ce-ce-ku-ce.
Ya yi ƙoƙarin kawo sauyi a tsarin Fadar Vatican da daƙile cin hanci da magance wasu muhimman ƙalubale da cocin ke fuskanta.
Yayin da aka yaba masa saboda tawali'u da sadaukarwarsa ga adalci na zamantakewa, shugabancinsa kuma ya jawo suka da turjiya daga masu ra’ayin ‘yan mazan jiya a ciki da wajen cocin.
Kafin rasuwarsa, ya kasance ɗaya daga cikin masu magana kan haƙƙin Falasɗinawa da sauran jama’ar da ake zalunta a faɗin duniya.
Comments
No comments Yet
Comment