Sport
Dollar
37,9365
-0.08 %Euro
41,1272
-0.07 %Gram Gold
3.786,8500
-0.64 %Quarter Gold
6.210,1600
0 %Silver
41,1000
-1.35 %"Ta yadda duniya ta kasance gidanmu gaba ɗaya, dole mu kasance masu fafutukar ceton wannan gidan namu daga wutar da ta mamaye shi," kamar yadda Emine Erdogan ta bayyana a shafinta na X.
Da take taya murnar ranar kawar da shara ta duniya, matar shugaban ƙasar Turkiyya Emine Erdogan ta buƙaci haɗin kan duniya wajen tabbatar da makoma mai ɗorewa.
"Turkiyya ƙasa ce da ke tunkarar duniya da zuciya ɗaya,” kamar yadda Erdogan ta bayyana ranar Lahadi a shafin X.
“Mun yi imanin cewa bil’adama katafaren iyali ɗaya ne a ƙarƙashin sama ɗaya.
“Za mu iya samun makoma mai ɗorewa ta hanyoyin yarjejeniyar inda duk ƙasashe za su taka rawa bai-ɗaya, ‘ba tare da an bar kowa a baya ba’,” in ji ta.
Matar shugaban ƙasar ta jaddada cewa kare muhalli nauyi ne da ya rataya a kan kowa, tana mai cewa, “Yadda duniya ta kasance gidanmu gaba ɗaya, dole mu kasance masu fafatukar kare wannan gidan namu daga wutar da ta mamaye shi.”
Ta kammala saƙonta da taya murnar zagoyawar ranar kawar da shara ta duniya tare da bayyana fatan samun “duniya mai cike da lafiya da zaman lafiya inda albarkatunmu za su ci gaba da kasancewa masu yawa.”
A shekarar 2022, Zauren MDD ya haɗa baki wajen amincewa da ƙudurin kawar da shara wanda Turkiyya ta gabatar, inda ta ayyana ranar 30 ga watan Maris a matsayin ranar kawar da shara ta duniya.
Matar shugaban ƙasar ta jagoranci ƙoƙarin Turkiyya kan kawar da shara da kuma yaɗuwarsa a duniya.
Comments
No comments Yet
Comment