Dollar

37,9310

-0.05 %

Euro

41,2266

0.41 %

Gram Gold

3.809,9500

0.27 %

Quarter Gold

6.332,2600

1.97 %

Silver

41,2200

-1.05 %

"Ba za mu ƙyale waɗanda suke ƙoƙarin yi wa kan iyakokin Syria zagon ƙasa tare da dawwamar da rashin zaman lafiya a kan iyakokinmu na kudu ba," in ji Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan.

Shugaban Turkiyya ya jaddada goyon bayan mutunta iyakokin ƙasar Syria a jawabinsa na ƙaramar Sallah

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce Turkiyya ba za ta lamunci ƙeta haƙƙin kan iyakokin ƙasar Syria tare da dawwamar da rikici a kan iyakar kudancin ƙasar ba.

A wani jawabin ƙaramar Sallah da ya yi ranar Lahadi – ƙarshen azumin watan Ramadan --Erdogan ya bayyana cewa Turkiyya  za ta “ci gaba da aikin da muka fara bisa manufarmu ta ‘Turkiyya ba tare da ta’addanci ba’ kuma daidai da tsare-tsarenmu.”

Ya yi gargaɗin cewa Ankara ba ta da “haƙuri mara iyaka” kan batun kuma yana sa ran ƙungiyoyin ta’addancin PKK/YPG su watse da kansu tare da “ajiye makamansu gabaɗaya ba tare da ɓata lokaci ba.”

A cikin kusan shekara 40 da ta shafe tana kai hare-haren ta’addanci kan Turkiyya, ƙungiyar PKK – wadda Turkiyya da Amurka da kuma Ƙungiyar Tarayyar Turai suka ayyana a matsayin ƙungiyar ta’addanci – ta yi sanadin mutuwar sama da mutum 40,000 ciki har da mata da yara da jarirai.

Ƙungiyar YPG/PYD, wadda ke kuma amfani da suna SDF, ita ce reshen PKK a Syria.

‘Yan ta’addan PKK suna yawan ɓuya a arewacin Iraƙi domin kitsa hare-hare a Turkiyya yayin da YPG/PYD  ta yi ƙoƙarin kafa wata hanyar ta’addanci a arewacin Syria  kusa da kan iyakar Turkiyya.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#