Sport
Dollar
38,2116
0.04 %Euro
44,0611
0.78 %Gram Gold
4.131,3200
1.34 %Quarter Gold
6.767,1400
0 %Silver
40,0400
0.3 %Tsawon kwanaki da dama, RSF na ci gaba da harba makaman roka a El-Fasher, wanda ya yi sanadiyar mutuwar ɗaruruwan mutane da jikkata wasu, a cewar hukumomin Sudan da Majalisar Ɗinkin Duniya.
Fararen hula bakwai ne suka mutu sannan wasu uku suka jikkata sakamakon luguden wuta da dakarun Rapid Support Forces (RSF) suka yi a El-Fasher, babban birnin lardin Darfur ta Arewa a yammacin Sudan, in ji rundunar sojin kasar a ranar Lahadi.
Sanarwar da rundunar sojin ta fitar ta ce, fararen hular da suka rasa matsugunansu a sansanin 'yan gudun hijira na Zamzam da sauran yankunan lardin Darfur na fuskantar "cin zarafin bil'adama da nuna wariya" daga mayakan na RSF da suka hada da toshe hanyoyi da satar dukiya.
Babu wani ƙarin haske daga RSF game da sanarwar sojojin.
Tsawon kwanaki da dama, RSF na ci gaba da harba makaman roka a El-Fasher, wanda ya yi sanadiyar mutuwar ɗaruruwan mutane da jikkata wasu, a cewar hukumomin Sudan da Majalisar Ɗinkin Duniya.
Wurin ayyukan jin ƙai maras aminci
Tun a watan Mayun shekarar 2024 ne birnin ya gamu da mummunan yaƙi tsakanin sojojin Sudan da RSF, duk da gargaɗin da ƙasashen duniya suka yi kan haɗarin da ke tattare da faɗa a El-Fasher, wadda ta kasance cibiyar ayyukan jin kai a dukkan jihohin Darfur biyar.
A farkon makon nan ne dai kungiyar RSF ta yi iƙirarin cewa ta ƙwace iko da sansanin 'yan gudun hijira na Zamzam da ke El-Fasher bayan wata arangama da dakarun soji. Aƙalla fararen hula 400 ne aka kashe sannan kusan 400,000 suka rasa muhallansu sakamakon faɗan, a cewar alƙaluman MDD.
Tun a ranar 15 ga Afrilu, 2023, RSF ke fafatawa da sojojin Sudan don samun iko a kasar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane a ɗaya daga cikin mafi munin rikicin jin kai a duniya.
Fiye da mutane 20,000 ne aka kashe ya zuwa yanzu, yayin da wasu miliyan 15 suka rasa matsugunansu, a cewar Majalisar Dinkin Duniya da hukumomin kasar. Bincike daga malaman Amurka, ya kiyasta adadin wadanda suka mutu ya kai kusan 130,000.
Comments
No comments Yet
Comment