Dollar

35,1761

-0.01 %

Euro

36,7640

0.01 %

Gram Gold

2.956,9600

-0.70 %

Quarter Gold

4.901,0500

-0.09 %

Silver

33,2100

-1.47 %

Continents

Categories

Dubban 'yan ci-rani ne ke yunkurin tsallakawa cikin teku daga gabar tekun Afirka a kowace shekara da fatan shiga Turai, galibi a suna ƙoƙrin yin haka ne a cikin kwale-kwale ko jirgin ruwa maras nagarta.

Mutum 70 sun yi ɓatan-dabo sakamakon kifewar jirgin ruwa a Morocco

Nutsewar wani jirgin ruwa ɗauke da 'yan ci-rani a Tekun Morocco a ranar 19 ga watan Disamba ya yi sanadin ɓacewar mutum 70, ciki har da 25 daga kasar Mali, in ji gwamnatin kasar a ranar Alhamis.

Kusan 'yan ci-rani 80 ne a kan jirgin wanda ke hanyarsa ta zuwa Sifaniya, "akwai matasan Mali 25 waɗanda aka gano ya rutsa da su" kamar yadda gwamnatin ta bayyana a cikin wata sanarwa.

Dubban 'yan ci-rani ne ke yunkurin tsallakawa cikin teku daga gabar tekun Afirka a kowace shekara da fatan shiga Turai, galibi a suna ƙoƙrin yin haka ne a cikin kwale-kwale ko jirgin ruwa maras nagarta.

Tafiya mai hatsari

Fiye da baƙin haure 10,400 ne suka mutu a kokarin isa Sifaniya tun daga shekarar 2024, ciki har da wani adadi mai yawa da ke kan hanyar zuwa tsibirin Canary, in ji wata kungiya mai zaman kanta ta Sifaniya, Caminando Fronteras a cikin wani rahoto a ranar Alhamis.

Hakan na nufin a matsakaicin lissafi aƙalla mutum 30 a rana.

A tafiya ta kusa-kusa, tsibirin na Canary na da nisan kilomita 100 daga gaɓar Tekun Arewacin Afirka.

Hanya mafi ƙanƙanta ta fara ne daga garin Tarfaya da ke kudancin Maroko zuwa Fuerteventura da ke tsibirin Canary.

Hanyoyin ruwa na Tekun Atlantika suna da matuƙar haɗari inda jiragen ruwa da dama waɗanda ake cikawa maƙil, waɗanda kuma ba su da kayayyakin aiki.

Wasu daga cikin jiragen ruwan da ke barin bakin ruwa a Afirka na da nisan kusan kilomita 1,000 daga tsibirin na Canary.

Mali ta jima tana fama da matsalolin tsaro tun daga shekarar 2012, inda take fuskantar hare-hare daga masu iƙirarin jihadi waɗanda ke da alaƙa da al-Qaeda, da kuma ƙungiyoyin 'yan aware.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa tun daga shekara ta 2014 zuwa yanzu fiye da bakin haure 16,400 ne suka mutu a kokarin shiga Turai daga Afirka, adadin da ya hada da wadanda ke kan hanyar zuwa tsibirin Canary.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet