Sport
Dollar
38,0104
0.16 %Euro
41,7696
-0.88 %Gram Gold
3.690,1100
-2.81 %Quarter Gold
6.293,2300
-0.18 %Silver
35,8900
-7.63 %NAFDAC ta sanar da cewa dole masu shaguna su cika wasu sharuɗa masu tsauri kafin sake buɗe shagunansu don kauce wa sake faruwar abubuwan da suka janyo aka rufe kasuwar.
Hukumar Kula da Ingancin Aabinci da Magunguna ta Ƙasa a Nijeriya (NAFDAC) ta umurci a sake buɗe kasuwar magunguna ta Bridgehead da ke Onitsha a jihar Anambra, wadda aka fi sani da Ogbo Ogwu, kana ta buƙaci ‘yan kasuwar da su sanya hannu kan wata yarjejeniya a hukumance da ƙungiyarsu.
Hukumar ta NAFDAC ta kuma sanar da cewa dole ne masu shagunan su cika sharuɗan gudanar da kasuwanci kafin buɗe shagunansu domin gudun sake faruwar lamarin da ya kai ga rufe shagunan tun farko.
NAFDAC ta bayyana hakan ne a ranar Laraba a wata sanarwa da ta fitar, ɗauke da sa hannun shugabar hukumar Farfesa Mojisola Adeyeye.
Kazalika, NAFDAC ta ce za a yi amfani da dokokin rarraba magunguna na baya nan-take, domin hukunta duk wanda aka kama da laifi.
An rufe kasuwar magunguna ta Onitsha Bridgehead wacce ta haɗa da Ogbo Ogwu da kuma wasu kasuwanni guda uku da ke maƙwabtaka da juna daga ranar 10 ga watan Fabrairu zuwa 7 ga Maris don gudanar da bincike kan harkokin saye da rarraba magunguna.
Comments
No comments Yet
Comment