Sport
Dollar
38,1137
0.18 %Euro
42,0543
-0.85 %Gram Gold
3.708,4600
-2.33 %Quarter Gold
6.293,2300
-0.18 %Silver
36,1600
-6.93 %Tsohon janar ɗin na soja wanda ya samu 'yanci daga masu garkuwa a ranar Laraba ya ce kuraye sun kewaye shi da sauran mutanen da aka yi garkuwa da su kwana daya gabanin sako su.
Tsohon shugaban Hukumar Yi Wa Ƙasa hidima (NYSC) a Nijeriya, Janar Maharazu Tsiga ya bayyana irin mummunan yanayin da ya shiga a yayin da yake tsare a hannu mutane da suka yi garkuwa da shi har tsawon kwanaki 56.
Janar ɗin mai ritaya, wanda ya samu ‘yanci daga masu garkuwa da mutane a ranar Laraba ya bayyana cewa kuraye sun kewaye shi tare da sauran mutanen da aka yi garkuwa da su kwana ɗaya gabanin a sako su, kamar yadda jaridar Punch da ake bugawa a Nijeriya ta rawaito.
A yayin da yake magana a Abuja a ranar Alhamis a yayin miƙa mutane 19 da aka ceto daga hannun masu garkuwa da mutanen ga iyalansu, Tsiga ya bayyana wahalhalun da shi da sauran mutanen suka sha yayin da suke tsare.
‘'Kwana guda kafin na bar wurin, a kan dutsen da nake, kawai, sai mu ka ga kuraye kewaye da mu suna yawo, suna neman abinci. Wane irin abinci suke nema? Mu, mutane,” a cewarsa.
Ya kara da cewa, waɗanda aka yi garkuwa da su suna yawan cin karo da macizai da kunamu yayin da suke tsare.
Jaridar Punch ta rawaito cewa Janar Tsiga ya bayyana yadda masu garkuwar suke yin amfani da manyan mutane don zame musu kariya daga hare-haren jirage sama da ake kai musu.
‘‘Duk lokacin da aka kai musu hari, sai su fito da mu don jirgin saman ya kai hari a kanmu. Amma da yake, Allah mai rahama ne - waɗanda kwanansu bai kare ba za su ci gaba da rayuwa,’’ in ji shi.
A cewarsa, masu garkuwa da mutanen sun yi imani cewa jami'an gwamnati masu kayan sarki suna da damar samun kudi, hakan ya sa suka kutsa gidansa ta hanyar amfani da abubuwan fashewa kana suka yi garkuwa da shi.
Comments
No comments Yet
Comment