Dollar

38,1137

0.18 %

Euro

42,0543

-0.85 %

Gram Gold

3.706,4600

-2.38 %

Quarter Gold

6.293,2300

-0.18 %

Silver

36,1500

-6.98 %

Dama a ranar Litinin biyu ga ƙaramar sallah wanda ya yi daidai da 31 ga watan Maris ne shafin makaranta na malamin ya sanar da cewa ba shi da lafiya har ma ta yi tsananin da bai iya fita jan salla da gabatar da huɗuba ba.

Allah Ya yi wa Dr Idris Dutsen Tanshi na Bauchi rasuwa

Allah Ya yi wa fitaccen malamin addinin Musulunci a Nijeriya Dr Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi rasuwa a cikin daren Juma’a.

Shafin makarantar malamin a Facebook ne ya tabbatar da rasuwar marigayin a cikin daren Juma’a bayan fama da ‘yar gajeriyar rashin lafiya.

Dama a ranar Litinin biyu ga ƙaramar sallah wanda ya yi daidai da 31 ga watan Maris ne shafin makaranta na malamin ya sanar da cewa ba shi da lafiya har ma ta yi tsananin da bai iya fita jan salla da gabatar da huɗuba ba.

Tuni kuma shafin mai suna ‘Zauren Dr. Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi’ ya wallafa sanarwar jana’izar malamin, inda ya ce za a gabatar da ita da misalin karfe 10:00 na safe a Masallacin Idi na Games Village da ke Bauchi.

Manyan malamai da ma Musulmai da dama a Nijeriya suna ta bayyana alhini da jimamin rasuwar Dr Dutsen Tanshi.

Ko a cikin watan Ramadana da ya wuce ɗin nan Dr Dutsen Tanshi ya gabatar da tafsirin karatun Kur’ani kamar yadda ya saba.

Wasiyya

A wasiyyar da ya taɓa bari a karatuttukansa, Dr Dutsen Tanshi ya haramta ɗaukar hoto a wajen jana’izarsa da zaman makoki da kuma turereniyar taɓ gawarsa da ma shiga maƙabarta da takalmi.

Kazalika Sheik Dutsen Tanshi ya shahara a fannin karantarwarsa musamman ta ɓangaren Tauhidi inda da yawa “suke masa kallon gwarzo marar tsoro.

Malamin ya yi suna sosai musamman a shekarun baya bayan nan saboda “taƙaddamar da ake yawan samu tsakaninsa da ko dai wasu malaman ko kuma hukumomi.”

Ya yi karatunsa na digiri a fannin Shari’ar Musulunci a Jami’ar Madina sannan ya yi karatun digirin-digirgir a fannin Fiƙihu a Sudan.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#