Dollar

38,1337

0.13 %

Euro

43,6872

1.39 %

Gram Gold

4.085,7300

3.3 %

Quarter Gold

6.731,9300

3.38 %

Silver

40,3700

1.95 %

Turkiyya da Somaliya sun sanya hannu kan wata yarjejeniya ta tarihi domin binciken man fetur da gas, wacce za ta bai wa Kamfanin Mai na Turkiyya (TPAO) damar yin aiki a fadin kasa da ya kai murabba'in kilomita 16,500.

Turkiyya da Somaliya sun saka hannu kan yarjejeniyar binciken fetur da iskar gas

Turkiyya da Somaliya sun fadada haɗin gwiwarsu a fannin makamashi ta hanyar sanya hannu kan yarjejeniyar bincike da samar da albarkatun mai.

Yarjejeniya ta bai wa Kamfanin Mai na Turkiyya (TPAO) damar fara binciken man fetur da iskar gas a cikin wasu yankuna guda uku da ke da faɗin kusan murabba’in kilomita 16,000 a Somaliya.

An sanya hannu kan yarjejeniyar ne a Ankara a ranar Alhamis, tsakanin Ministan Makamashi da Albarkatun Ƙasa na Turkiyya, Alparslan Bayraktar, da Ministan Man Fetur da Albarkatun Ma’adanai na Somaliya, Dahir Shire Mohamed.

Wannan mataki ya zama wani sabon shafi a haɗin gwiwar ƙasashen biyu bayan yarjejeniyoyin da aka yi a baya kan binciken albarkatun teku.

Minista Bayraktar ya tabbatar da cewa kamfanin makamashin Turkiyya, TPAO, zai fara ayyukan bincike a yankunan da aka ware cikin watanni masu zuwa.

“Da wannan yarjejeniya, an kafa haɗin gwiwa a ɓangaren bincike a ƙasa,” in ji Bayraktar. “Da farko, za a gudanar da binciken yanayin ƙarfin ƙasa, sannan za a fara haƙa don gano da kuma fitar da man fetur da iskar gas.”

Wannan yarjejeniya ta biyo bayan wata yarjejeniyar samarwa da raba abin da aka samu, da aka sanya wa hannu a watan Yulin 2024, wadda ta shimfida harsashin faɗaɗa ayyuka a fannin albarkatun Somaliya.

Bayraktar ya kuma bayar da sabbin bayanai kan kokarin Turkiyya a fannin binciken albarkatun teku a Somaliya.

Jirgin binciken yanayin ƙasa na Oruc Reis yana aiki a cikin wasu yankunan teku guda uku da ke da fadin murabba’in kilomita 15,000, inda ake gudanar da binciken yanayin ƙasa da fasahar 3D.

“A halin yanzu, aikin ya kai kashi 78 cikin 100,” in ji Bayraktar. “Muna sa ran kammala binciken a watan Mayu, sannan mu yanke shawara kan matakin haƙowa bisa bayanan da aka tattara.”

Fannin ma’adinai

Turkiyya da Somaliya suna shirin ƙarfafa haɗin gwiwarsu. “Muna fatan shiga sabon mataki a dangantakarmu ta hanyar ƙaddamar da ayyuka masu ma’ana a fannin ma’adinai,” in ji Bayraktar.

Minista Dahir ya jaddada muhimmancin wannan yarjejeniya, yana mai cewa ta ɗaga matsayin dangantakar ƙasashen biyu zuwa sabon matsayi. “Za mu bunƙasa albarkatun cikin gida na Somaliya tare da neman sakamako mai amfani ga ƙasashen biyu,” in ji shi, yana mai cewa ana sa ran kamfanonin ma’adanai na Turkiyya za su shiga Somaliya da zarar an samar da tsare-tsare na doka da suka dace.

Bayraktar ya kuma sanar da cewa Turkiyya za ta karɓi baƙuncin Taron Ƙasa da Ƙasa kan Albarkatun Duniya a Istanbul a ranar 2 ga Mayu, ƙarƙashin jagorancin Shugaba Recep Tayyip Erdogan.

Wannan taro zai taro ministoci da kamfanonin makamashi daga sassa daban-daban na duniya don inganta haɗin gwiwa a fannin man fetur da iskar gas, da ma’adanai.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#