Sport
Dollar
38,1327
0.12 %Euro
43,6679
1.4 %Gram Gold
4.081,0300
3.18 %Quarter Gold
6.731,9300
3.38 %Silver
40,3500
1.91 %Turkiyya da Indonesia sun sake jaddada alaƙarsu ta hanyar shirin sake gina Gaza da kuma inganta harkokin kasuwanci zuwa dala biliyan 10.
Shugaban Ƙasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya bayyana cewa Ankara za ta ci gaba da aiki tare da Indonesiya wajen sake gina Gaza da kuma kare al'amuran Falasɗinu.
Erdogan ya yi wannan jawabi ne yayin wani taron manema labarai tare da takwaransa na Indonesiya, Prabowo Subianto, a babban birnin ƙasar, Ankara.
Shugaban na Turkiyya ya kuma yaba da matsayin Indonesiya kan batun Falasɗinu.
Game da dangantakar kasashen biyu, Erdogan ya bayyana cewa shi da Prabowo sun tattauna matakan da za a iya ɗauka don ƙara haɓaka cinikayya tsakanin ƙasashen zuwa burinsu na dala biliyan 10, "ta hanyar daidaito da kuma amfanin juna."
Tun da farko, Erdogan ya tarbi Prabowo da wani bikin maraba na musamman a Fadar Shugaban Ƙasa.
Shugabannin biyu sun gudanar da taron tattaunawa na ƙawance sun jagoranci tattaunawar tsakanin tawagogin kasashen biyu.
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Hakan Fidan da Ministan Tsaron Ƙasa, Yasar Guler da Ministan Al’adu da Yawon Buɗe Ido, Mehmet Nuri Ersoy da Ministan Kuɗi, Mehmet Simsek, da wasu jami’ai sun halarci bikin maraban.
Prabowo ya fara ziyarar aiki a Turkiyya ranar Laraba, kuma ana sa ran zai halarci Babban Taron Diflomasiyya na Antalya na kwanaki uku, wanda zai fara ranar Juma’a.
Comments
No comments Yet
Comment