Dollar

38,1588

0.3 %

Euro

43,6101

1.61 %

Gram Gold

3.958,7400

2.25 %

Quarter Gold

6.529,2600

2.67 %

Silver

39,4700

3.6 %

Rundunar sojin Sudan ta yi iƙirarin ƙwace Souq Libya, ɗaya daga cikin manyan kasuwannin Sudan.

Sojojin Sudan sun ƙwace wata babbar kasuwa a Omdurman a yayin da suke ci gaba da mamaya

Rundunar sojin Sudan ta ce dakarunta sun ƙwace wata babbar kasuwa a birnin Omdurman na kusa da Khartoum babban birnin ƙasar, wadda a baya take hannun dakarun Rapid Support Forces (RSF) da suka kwashe shekaru biyu suna gwabza yaƙi da su.

Sanarwar da rundunar sojin Sudan ta fitar ranar Asabar game da ƙwace kasuwar na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan ta yi iƙirarin samun nasara kan dakarun RSF tare da ƙwace galibin sannan birnin.

Rundunar ta ce yanzu haka dakarunta ne suke riƙe da Souq Libya, kasuwar da ke yammacin Omdurman, bayan sun ƙwace makamai da dakarun RSF suka bari yayin da suka tsere daga yankin.

Souq Libya tana ɗaya daga cikin manyan kasuwa da aka fi hada-hada a Sudan.

Tuni dai sojojin suka ƙwace Omdurman, inda ake da manyan sansanoni biyu na sojojin ƙasar. Da alama sun sha alwashin ƙwace ɗaukacin yankin babban birnin, wanda ya haɗa da birane uku Khartoum, Omdurman da Bahri, waɗanda Kogin Nilu ya raba.

Rundunar RSF ba ta ce komai ba game da nasarar da dakarun rundunar sojin Sudan suka samu a Omdurman, inda har yanzu suke riƙe da wasu sassa.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#