Sport
Dollar
37,9972
0.02 %Euro
41,6773
-0.12 %Gram Gold
3.650,1200
-1.63 %Quarter Gold
6.185,6400
-1.34 %Silver
36,5000
0.96 %Zagaye na biyu na tattaunawa tsakanin Turkiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa zai yi nazari ne kan ɓangarorin haɗin kai domin inganta ci-gaban Afirka da kuma zuba jari.
Turkiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa za su yi taro karo na biyu kan Afirka a Abu Dhabi ranar Litinin, kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen Turkiyya ta tabbatar.
Mataimakin ministan harkokin wajen Turkiyya Burhanettin Duran da kuma ƙaramin ministan harkokin wajen Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Shahbut bin Nahyan Al Nahyan, za su jagoranci taron.
Tattaunawar za ta mayar da hankali ne kan ababen da ke faruwa a Afirka tare da nazari kan fannonin da za a iya samun haɗin kai na tattalin arziƙi da zuba jari a nahiyar.
An yanke shawarar zaman tattaunawa game da Afirka ne a a lokacin da Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya ziyarci Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa a watan Fabrairun shekarar 2022, bayan wata ganawa tsakanin ministocin harkokin wajen ƙasashen biyu.
Bayan cim ma matsayar, an yi zaman tattaunawa tsakanin Turkiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa game da Afirka a birnin Ankara ranar 10 ga watan Oktoba na shekarar 2023.
Comments
No comments Yet
Comment