Dollar

38,0194

0.25 %

Euro

42,0550

1.11 %

Gram Gold

3.677,7500

1.12 %

Quarter Gold

6.191,9000

0 %

Silver

36,4800

0.23 %

Numan Kurtulmus ya jaddada cewa dole ne ƙasashen duniya su tunkari rashin daidaito, da yaƙe-yaƙe da rikicin siyasa ke ƙara girmama, tare da kuma kudirce tabbatar da adalci, da kare daraja da mutunci da tafiya da kowa.

Shugaban Majalisar Dokokin Turkiyya ya yi kira ga adalci a tsarin tafiyar da duniya

Shugaban Majalisar Dokokin Turkiyya Numan Kurtulmus ya yi kira ga a yin garembawul ga tsarin siyasa da tattalin arzkin duniya, yana mai cewa tsarin da ake a kai a yanzu, wanda ke biyan buƙatun wasu ‘yan tsiraru, na tattare da tsagwaron rashin adalci, da raunana kasashe, da ingiza duniya ga rikicike-rikice.

Da yake jawabi a wajen Taron Kungiyar Majalisun Dokoki karo na 150 (IPU) a Tashkent, Uzbekistan a ranar Lahadi, Kurtulmus ya jaddada cewa dole ne ƙasashen duniya su tunkari yadda rashin daidaito, da yaƙe-yaƙe da rikicin siyasa ke kara girmama, tare da kuma kudirce tabbatar da adalci, da kare daraja da mutunci da tafiya da kowa.

Kurtulmus ya yi gargaɗin cewa tsarin duniya da aka gina shi kan yadda wasu tsirarun ƙasashe masu ƙarfi sukr danniya a harkar siyasa da ta tattalin arzikin sauran kasashen, ba mai dorewa ba ne. Ya ce yadda tsarin ya gaza biyan bukatun mafi yawan jama’a ya taimaka wajen janyo rikici, da shugabanci mai rauni da ƙaruwar hatsaniya a duniya.

“Har ma abubuwan da ke afkuwa a Falasdinu, idan muka ajiye sauran ibtila’i’in duniya a gefe guda, na bayyanawa ƙarara cewa akwai buƙatar sabon tsari da zubin siyasa da tattalin arziki,” in ji shi.

‘Dole majalisun dokoki su zama marasa iyaka’

Shugaban ya kuma bayyana damuwa kan irin rawar da shafukan sadarwa na intanet da kafofin yaɗa labarai ke takawa wajen manubar jan ra’ayin al’umma. Ya yi gargaɗin cewa abubuwan da ake yaɗa wa waɗanda alƙaluman kwamfuta ke gabatarwa na lalata shiga dimokuradiyya ta hanyar jujjuya labarai da matse yanayin samun bayyananniyar muhawara.

“Idan mu, a matsayin mu na ‘yan majalisa, ba mu sanya baki a wannan tsarin ba, to za mu dinga gudu a duniyar da ake tauye batun dimokuradiyya,” Kurtulmus ya yi gargadi, yana bayyana alhakin da ke kan ‘yan majalisa na kare tubalan dimokuradiyya.

Kurtulmus ya karafafa cewa a yabzu, Majaisun Dokoki ba iyakacin batutuwan cikin gida za su kalla ba, sannan su kalli kalubalan da duniya ke fuskanta. Ya jaddada cewar al’amura irin su diflomasiyyar ƙasa da ƙasa, da rikicin yankuna da rashin adalci a fannin tattalin arziki na yin tasiri sosai kan batutuwan da suka shafi kasashe, a saboda haka suna bukatar babban matakin siyasa.

Ya yi kira ga majalisun dokoki da su rungumi wata manufar duniya ta zaman lafiya, da hadin kai, da tattaunawa, maimakon koyaushe su dinga ƙoƙarin magance rikice-rikice.

Gaza ‘jarrabawa’ ga ƙasashen duniya

Da yake waiwayawa ga yaƙin Gaza, Kurtulmus ya la’anci hare-haren da Isra’la ke kai wa, wanda suka kashe sama da Falasdinawa 50,600 da janyo rikicin jin kai mafi muni a tarihin zamanin nan.

“Abin takaici, babu wata hukuma a duniya da ke yin wani abu ko take iya kataɓus wajen dakatar da wannan kisan kiyashi, da mummunan laifin da ake yi wa bani adam,” in ji shi, yana mai bayyana halin ko-in-kula da duniya ke nunawa a matsayin wanda bai isa ba kuma na rashin halayya mai kyau.

Ya bayyana rikicin a matsayin wani lokaci da ke bayyana nau’in ƙasashen duniya, yana mai cewa rikicin na bayyana buƙatar sake gina tsari da zai kare rayukan fararen hula da ba su ji ba ba su gani na ba, tare da tabbatar da adalci.

Kira ga majalisun dokoki da su dauki matakai

A yayin rufe jawabin nasa, Kurtulmus ya buaƙci shugabannin majalisun dokokin ƙasashen duniya da su dauki matakin samar da tsarin tafiyar da duniya mai adalci da zai tafi da kowa. Ya bayyana cewa kokarin zuba jari a ilimi, da habaka adalcin zamantakewa, da gina tsarin tattalin arziki zai tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

“Ina gayyatar dukkan mu, dukkan majlisun dokokin duniya, da mu yi aiki tare don samar da tsarin siyasa da tattalin arziki sabo wanda zai tabbatar da adalci,” in ji shi. “Aikin da za mu yi a wannan ɓangare zai bayar da gudunmawa sosai ga ‘yan’adam.”

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#