Dollar

38,0020

0.05 %

Euro

41,6564

-0.1 %

Gram Gold

3.698,9700

-0.31 %

Quarter Gold

6.191,9000

-1.24 %

Silver

36,8200

1.85 %

Mali ta zargi Aljeriya da harbo jirginta marasa matuki da ke sa ido a kan iyakokinta a makon da ya gabata.

Nijar, Mali, da Burkina Faso sun kira jakadunsu daga Algeria

Ƙasar Mali ta zargi makwabciyarta Aljeriya da harbo daya daga cikin jiragenta marasa mutuki da ke sa ido a kusa da kan iyakokinsu, kamar yadda wata sanarwa da ministan tsaron ƙasar ya karanta a gidan talabijin na ƙasar a ranar Lahadi.

Kasar wadda ke yankin yammacin Afirka da kawayenta Burkina Faso da Nijar za su kira jakadunsu daga Aljeriya domin tattaunawa kan lamarin, a cewar wata sanarwar ta haɗin gwiwa ta daban da kasashen suka fitar a ranar Lahadi.

Mali ta ce an gano tarkacen jirgin mara matuki a nisan kilomita 9.5 kudu da kan iyaka da Aljeriya bayan da aka harbo shi cikin dare tsakanin ranar 31 ga Maris da 1 ga Afrilu.

‘Sabawa doka’

Gwamnatin kasar ta ce ta kammala "cikakkiyar bincikenta kan cewa an lalata jirgin mara matuki na sojojin Mali ne a wani mataki na kiyayya da gwamnatin Aljeriya ta shirya."

 A sanarwar hadin gwiwa da ƙasashen Sahel din uku suka fitar, sun bayyana cewa, sun yi matukar yin Allah wa-dai da matakin ‘‘saba doka na gwamnatin Aljeriya.’’

Ma'aikatar tsaron Aljeriya a ranar 1 ga watan Afrilu ta ce sojojin kasar sun harbo wani jirgin sama marasa matuki dauke da makami wanda ya keta sararin samaniyar kasar ta arewacin Afirka kusa da Tinzaouaten, yankin da ke kan iyaka da kasar, ba tare da bayar da wani karin bayani ba.

Sai dai a wata sanarwar da rundunar sojin Mali ta fitar ta ce, daya daga cikin jirginta mara matuki ya yi hatsari a lokacin da yake aikin sa ido.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#