Sport
Dollar
38,1588
0.3 %Euro
43,6101
1.61 %Gram Gold
3.958,7400
2.25 %Quarter Gold
6.529,2600
2.67 %Silver
39,4700
3.6 %Wani jami'i ya ce da alama wanda ya yi harbin ɗan Alshabab ne da ya yi shigar burtu, kuma tuni aƙa ƙaddamar da bincike.
Wani mutum sanye da kayan soja ya harbe wani babban kwamanda na sojojin Somaliya Laftanar Kanar Nuur Farey a ranar Asabar, in ji wani jami'i.
Wani jami'in tsaro a yankin, Bulle Ali, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa an kashe kwamandan Rundunar 14 ga Oktoba ta Sojojin Somaliya yayin da yake jawabi ga sojoji a wajen garin Afggoye, yankin Shabelle.
Garin Afgooye yana da nisan kilomita 30 kudu maso yammacin babban birnin ƙasar, Mogadishu.
Ya ce an kama wanda ya kai harin, wanda ake zaton ɗan kungiyar al-Shabaab ne da ya yi shigar burtu cikin sojoji, kuma ana gudanar da bincike.
Sake kwato garuruwa
Rundunar 14 ga Oktoba, wadda aka ƙirƙira domin tunawa da waɗanda suka rasa rayukansu a harin ta'addanci mafi munin a tarihin Somaliya, tana jagorantar ƙoƙarin sake ƙwato garuruwan da ke hannun ƙungiyar ta'addanci ta al-Shabaab a yankin Shabelle.
A ranar 14 ga Oktoba, 2017, wani bam da aka ɗana a mota ya tashi a wata mahaɗar hanyoyi mai cunkoson jama'a a Mogadishu, inda ya kashe mutane 587.
“Cike da baƙin ciki, ina miƙa ta'aziyyata ga iyali da dangi da Sojoji da duk al'ummar Somaliya, bisa rasuwar Laftanar Kanar Nur Mohamed Gaabow (Nuur Farey), Kwamandan Rundunar 14 ga Oktoba na Sojojin Somaliya,” in ji Birgediya Janar Abdullahi Ahmed Sheikh, tsohon kwamandan sojoji na musamman, a shafinsa na X.
Babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kisan nan take.
A watan Nuwamba, wasu sojojin ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa huɗu da wani jami'in soja na Bahrain sun rasa rayukansu a wani hari da aka kai musu a sansanin soja a babban birnin Somaliya, Mogadishu. Kungiyar al-Shabaab ta ɗauki alhakin harin, tana mai cewa ɗaya daga cikin mambobinta ne ya kai shi.
Comments
No comments Yet
Comment