Sport
Dollar
38,1137
0.18 %Euro
42,0543
-0.85 %Gram Gold
3.708,4600
-2.33 %Quarter Gold
6.293,2300
-0.18 %Silver
36,1600
-6.93 %Babban Hafsan Hafsoshin Tsaro, ya bayyana shirin a matsayin wani muhimmin mataki ga Njieriya wajen dogaro da kai a fasahar tsaro da inganta tsaron ƙasa.
Rundunar sojin Nijeriya ta ƙaddamar jiragen yaƙi marasa matuƙi da aka ƙera a Nijeriya a karon farko kuma mafi girma a ƙasar da Afirka baki ɗaya, wanda aka ƙera tare da haɗin gwiwar kamfanin Briech USA na Amurka
A yayin taron kaddamar da jirgin da aka yi a hedikwatar Briech UAS da ke Abuja a ranar Laraba, Babban Hafsan Hafsoshin Tsaro ƙasar, Janar Christopher Musa ya bayyana shirin a matsayin wani muhimmin mataki a tafiyar Njieriya wajen dogaro da kai a fasahar tsaro da inganta tsaron ƙasa.
Christopher Musa ya bayyana jiragen a matsayin waɗanda za su kawo sauyi wajen tunkarar barazanar matsalolin tsaro, inda ya jaddada muhimmacin samar da hanyoyin tsaro na soji a cikin gida, da kuma ƙalubale a siyasar duniya wajen samar da kayyakin tsaro.
‘‘Jiragen za su taka muhimmiyar rawa wajen haɓaka ayyukan sojojinmu, musamman a duniyar da samar da kayyakin aikin soja na zamani ke cike da ƙalubale saboda siyasar duniya.’’
"Idan ba ku samar da abin da kuke buƙata ba, za ku kasance a ƙarƙashin wasu, ko da kuna da albarkatun kuɗi don samun su," in ji shi.
Kazalika, ya ƙara da cewa jiragen za su taimaka wa Nijeriya wajen daukar matakan gaggawa don fuskantar kalubalen tsaro, tare da rage dogaro da kayayyakin ƙasashen waje.
Comments
No comments Yet
Comment