Sport
Dollar
35,4576
-0.07 %Euro
36,4924
-0.29 %Gram Gold
3.058,8200
0.18 %Quarter Gold
5.028,7800
0.82 %Silver
34,6400
1.52 %An ayyana Chapo a matsayin wanda ya lashe zaɓen da kashi 65 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa, yayin da babban abokin hamayyarsa Venancio Mondlane ke biye da shi da kashi 20 cikin 100.
An rantsar da Daniel Chapo a matsayin shugaban ƙasar Mozambique ranar Laraba bayan an shafe watanni ana tashin hankalin bayan zaɓe inda wata ƙungiya mai zaman kanta ta ce an kashe fiye da mutum 300.
Yayin da ya sha alwashin "sadauƙar da dukkan ƙarfina wajen karewa da kawo ci-gaba da kuma ƙarfafa haɗin kan ƙasa", Chapo, mai shekara 48, ya tsawaita mulkin shekara 50 da jam’iyyarsa ta Frelimo ke yi a ƙasar Afirkar mai arziƙin gas.
Ɗan takarar jam’iyyara hamayya Venancio Mondlane ya yi iƙirarin cewa an tafka maguɗi a zaɓen na watan Oktoba.
Tituna a babban birnin ƙasar Maputo sun kasance tamkar ba kowa inda shaguna suke a rufe ko domin rashin amincewa ko kuma domin tsoron tashin hankali yayin da Chapo yake fara wa’adinsa na shekara biyar.
An gudanar da jerin zanga-zanga a ƙasar da ke kudu maso gabashin Afirka tun ranar 21 ga watan Oktoba lokacin da hukumar zaɓen ƙasar ta ayyana Chapo a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa.
Rantsar da shugaban ƙasa
Lucia Ribeiro, shugabar babbar kotun ƙasar, ce ta rantsar da Chapo, wanda a baya ya yi gwamna a lardin Inhambane.
Ranar 23 ga watan Disamba, kotun ta tabbatar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasar.
Manyan jam’iyyun adawar Mozambique National Resistance Movement da kuma Mozambique Democratic Movement sun ƙaurace wa bikin rantsar da shugaban ƙasar.
An ayyana Chapo a matsayin wanda ya yi nasara ne da ƙuri’u kashi 65 cikin 100, yayin da babban abokin hamayyarsa da ke binsa Venancio Mondlane ya samu kashi 20 na ƙuri’un, in ji kotun.
An rantsar da sabuwar majalisar dokokin ƙasar mai ‘yan majalisu 250 ranar Litinin a lokacin da aƙalla mutum shida suka mutu a yayin zanga-zanga, sakamakon matakan da ake zargin ‘yan sanda sun ɗauka.
Zanga-zangar ‘yan hamayya
Mondlane ya riga ya yi kira da a yi yajin aiki na ƙasa kafin bikin rantsarwar kuma ya yi barazanar amfani da zanga-zanga a kullum domin yin ƙafar-ungulu ga sabuwar gwamnatin.
Mondlane, wanda ya yi kira da a yi zanga-zanga a lokacin da yake gudun hijirar da ya ƙaƙaba wa kansa a Afirka ta Kudu, ya koma ƙasar a makon jiya kuma ya sha alwashin naɗa kansa a matsayin shugaban ƙasa.
An ƙwace takardun tafiyarsa, in ji lauyansa.
Tashin hankalin da ake a faɗin ƙasar ya haddasa ƙwace da katse kasuwancin ƙetare da kuma lalata gine-ginen gwamnati.
Jerin zanga-zangar, in ji ƙungiyar Plataforma Decide da ke sa ido kan zaɓe, ya kashe mutum 300 a ƙasar da Portugal ta yi wa mulkin-mallaka tare da sa dubban mutane su je neman mafaka a ƙasashe maƙabta.
Comments
No comments Yet
Comment