Dollar

38,1343

0.12 %

Euro

43,6051

1.3 %

Gram Gold

4.076,4700

3.06 %

Quarter Gold

6.731,9300

3.38 %

Silver

40,3300

1.85 %

Jami’ai daga Mali da Nijar da Burkina Faso sun tattauna kan matsalolin yankin ciki har da na ta’addanci da tashin hankali na siyasa da kuma dangantakar da ta yi tsami da ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS).

An tattauna kan matsalolin yankin Sahel na Afirka a Taron Diflomasiyya a Antalya

Tattaunawa mai taken "Sahel: Makomar haɗin kai na yanki " an yi ta ne a Taron Diflomasiyyar Antalya inda ministocin harkokin wajen ƙasashen Mali da Nijar da kuma Burkina Faso suka halarta.

Ministocin harkokin wajen sun haɗa da ministan harkokin waje da haɗin kai na ƙetare na Mali, Abdoulaye Diop, da ministan harkokin waje da haɗin kan ƙetare da lamuran ‘yan Nijar a ƙetare, Bakary Yaou Sangaré, da kuma ministan harkokin waje da haɗin kai na ƙetare da kuma lamuran ‘yan Burkina Faso a ƙetare Karamoko Jean Marie Traoré.

 

Kauce wa ƙasashen Yamma masu ƙarfi

Ministan harkokin waje da haɗin kai na Mali Abdoulaye Diop ya ce ƙungiyar haɗin kan Sahel AES na fuskantar hare-hare masu barazana ga wanzuwawar ƙasashen: inda take yaƙi da ta’addanci da kuma barazanar juyin mulki na sojoji.

“Ƙasashenmu a buɗe suke kuma shirye suke domin aiki da sauran ƙasashen yankin. A shirye muke domin aiki kan haɗin kan yanki,” in ji Diop, yana mai ƙarawa da cewa al’umar Afirka al’umma ce ta daban.

Ya jaddada cewa ƙungiyar AES ba ta mayar da hankali kan lamuran soji kawai ba, amma tana da niyyar samar da damarmaki ga matasa domin hana kwararar baƙin-haure da kuma rauni ga hare-haren ta’addanci.

Diop ya soki takunkumin da ƙasashen yammacin duniya suka ƙaƙaba musu. “A ‘yan shekarun nan, mun gano cewa wasu ƙasashe masu ƙarfi na yammacin duniya suna ƙoƙarin ƙaƙaba takunkumi kan ƙasashenmu waɗanda ba sa samun makaman soji.”

“Wannan shi ya sa muka koma ga ƙasashe irin su Turkiyya da China da kuma Rasha,” in ji shi, yana mai nuna cewa waɗannan ƙasashen sun taimaka wajen samar da makaman da ake ɓukata – ba a kyauta ba, amma ta hanyoyin saya.

Ya soki Majalisa Ɗinkin Duniya (MDD) kan rashin ɗaukar mataki a Mali.

“Ya kamata MDD ta daina ƙirga yawan waɗanda suka mutu ta fara ceton rayuka,” in ji Diop. “Ba su yi komai ba wajen yaƙar ta’addanci a ƙasarmu.”

Suka ga ECOWAS

Ministan harkokin waje da haɗin kan ƙetare da kuma lamuran ‘yan Nijar a ƙetare Bakary Yaou Sangare, ya soki ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) kan bijire wa ƙa’iodojin da aka kafa ta a kai, yana mai cewa ta mayar da hankali kan ababen da ba su da alaƙa da lafiyar mambobinta. “Wannan ne ya sa muka yanke hukuncin ficewa,” in ji shi.

Ya kuma yi iƙirarin cewa janye sojojin ƙetare, ciki har da na Faransa, ya katse hanyoyin samun kuɗin ƙungiyoyin ‘yan ta’adda. “Yanzu hare-hare na raguwa kuma mace-mace na raguwa. Yaƙi ne na tsawon lokaci, amma ci-gaba a zahiri yake,” in ji shi.

Sangare ya bayyana muhimmiyar rawar da Turkiyya ke takawa a matsayin babbar mai taimakawa wajen yaƙi da ta’addanci, ya kuma bayyana gamsuwarsa da gudunmawar da Turkiyya ke bayarwa.

Burkina Faso na ganin alamun farfaɗowa

Ministan harkokin waje da haɗin kai na yanki da kuma lamuran ‘yan Burkina Faso a ƙetare, Karamoko Jean Marie Traore, ya ce ƙasarsa, wadda a shekarar 2022 ‘yan ta’adda ne ke iko da kashi 50 cikin 100 na ƙasar a halin yanzu ƙasar ta ƙwato kashi 71 cikin 100 na ƙasar.

Ya bayyana ayyukan ci-gaba a matsayin hujjar yadda tsaro ke ƙara inganci. “A cikin wannan shekarar kawai, mun buɗe sama da masana’antu biyar,” in ji shi. “Idan da gaske ƙasar ba ta da tsaro, babu wanda zai zuba jari.”

Ya jaddada cewa ga duka ƙasashen uku --Burkina Faso da Mali da Nijar – haɗin kai da Turkiyya ya zarce ɓangaren soji kawa zuwa dukkan ɓangarorin ci-gaba.

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#