Sport
Dollar
38,1246
0.1 %Euro
43,3620
0.63 %Gram Gold
3.970,9900
0.4 %Quarter Gold
6.511,6500
0 %Silver
39,6100
0.03 %Gwamnatin Ghana ta ce dole ne 'yan ƙasashen waje su bar kasuwar cinikin zinari ta ƙasar nan da 30 ga Afrilu ko da yake za su iya neman dama "domin saye ko dillancin zinari kai-tsaye daga hukumar GoldBod," in ji sanarwar.
Ghana ta bayar da umarni ga waɗanda ba ‘yan ƙasa ba su fita daga kasuwannin sayar da zinari na ƙasar zuwa ƙarshen watan nan.
Gwamnatin ce ta bayyana hakan a ranar Litinin a yunƙurinta na ƙara haɓaka sayen zinari daga ƙananan masu haƙar ma’adinai, da kuma ƙara adadin kuɗin shiga da daƙile fasa-kwauri.
A halin yanzu, ƙasar ta Afirka wadda ke kan gaba ta ɓangaren samar da zinari, tana ƙoƙarin sauya tsarin da ake da shi wanda kamfanoni na cikin gida da waje masu lasisi kan iya sayen zinari daga ƙananan masu haƙar ma’adinai.
A ƙarƙashin sabon tsarin, sabuwar hukumar da aka kafa ta sa ido kan haƙar zinarin mai suna GoldBod ita ce a halin yanzu ke da alhakin saye da sayar da zinarin da ƙananan masu haƙar ma’adinai, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Dole ne 'yan ƙasashen waje su bar kasuwar zinari ta ƙasar nan da 30 ga Afrilu ko da yake za su iya neman dama "domin saye ko dillancin zinari kai-tsaye daga GoldBod," in ji sanarwar.
Ministan Kuɗin Ghana Cassiel Ato Forson a watan Janairu ya bayyana cewa, samar da GoldBod zai bai wa Ghana damar cin gajiyar sayar da gwal tare da tabbatar da daidaiton kuɗin ƙasar.
Zinarin da Ghana ke fitarwa ya ƙaru da kashi 53.2 a shekarar 2024 zuwa dala biliyan 11.64, wanda zinari na kusan dala biliyan 5 ya fito ne daga wurin ƙananan masu haƙo ma’adinai da ke da lasisi.
Farashin zinari ya yi tashin gwauron zabi ranar Juma'a inda ya kai dala 3,200 kan kowane oza a karon farko.
Comments
No comments Yet
Comment