Sport
Dollar
38,1250
0.1 %Euro
43,2789
0.57 %Gram Gold
3.972,2900
0.43 %Quarter Gold
6.511,6500
0 %Silver
39,6300
0.08 %Hotunan tauraron ɗan'adam daga kamfanin fasaha na Maxar sun nuna yadda gine-gine ke ƙonewa tare da yadda hayaƙi ya turnuƙe sansanonin gudun hijira.
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa alkaluman farko daga majiyoyin kasar sun nuna cewa fiye da fararen hula 400 ne aka kashe a fadan da aka gwabza a ranar Juma’a da Asabar a kusa da sansanonin ‘yan gudun hijira na Zamzam da Abu Shouk da kuma garin Al Fasher da ke arewacin Darfur.
Wannan ya hada da jami’an agaji 10 na ƙungiyar bayar da agaji ta Relief International, waɗanda aka kashe a lokacin da suke gudanar da aikin daya daga cikin cibiyoyin lafiya na ƙarshe da suka rage a sansanin Zamzam, in ji kakakin Majalisar Dinkin Duniya.
Tsakanin Alhamis da Asabar ɗin makon jiya, ofishin kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya “ya tabbatar da kashe mutane 148,” in ji mai magana da yawun ofishin wato Ravina Shamdasani.
“Sai dai waɗannan kaɗan ne a cikin alƙaluma sakamakon har yanzu ana ci gaba da bincike,” in ji ta, inda ta ce adadin bai haɗa da waɗanda aka kashe a rikicin jiya ba”.
“Wasu majiyoyi masu ƙarfi sun ruwaito cewa fiye da mutum 400 aka kashe,” in ji ta.
Kalaman nata na zuwa ne bayan babban jami'in kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya Volker Turk ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa "manyan hare-haren ... sun fito fili karara sakamakon rashin daukar mataki da kasashen duniya ke yi, duk kuwa da gargadin da na yi na kara shigar hadari ga fararen hula a yankin".
"Daruruwan fararen hula, da suka hada da akalla ma'aikatan jin kai tara ne aka bayar da rahoton kashe su," in ji shi, yana mai gargadin cewa "hare-haren sun kara munana rikicin jin kai a wani birni da ke fama da mummunan harin RSF tun watan Mayun bara".
Tsakanin gidaje 60,000 zuwa 80,000—ko kuma mutane 400,000—sun rasa matsugunansu daga sansanin Zamzam na Sudan da ke Arewacin Darfur bayan da dakarun RSF suka karbe shi, a cewar bayanai daga Hukumar Kula da Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya.
Comments
No comments Yet
Comment