Sport
Dollar
37,9512
0.01 %Euro
42,0673
1.99 %Gram Gold
3.795,5800
-0.82 %Quarter Gold
6.304,8300
-0.43 %Silver
39,0300
-5.81 %Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan zai halarci taron Ƙungiyar Tsaro ta NATO wanda zai mayar da hankali kan sha'anin tsaro da yaƙin Ukraine da kuma haɗin gwiwa da abokan huldar Asiya da tekun Pasifik.
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan zai halarci taron ministocin harkokin wajen ƙungiyar tsaro ta NATO da za a yi a Brussels daga ranar 3 zuwa 4 ga watan Afrilu, kamar yadda majiyoyin diflomasiyya suka bayyana.
Taron dai na zuwa ne gabannin taron kolin Ƙungiyar Tsaro ta NATO da za a yi a watan Yuni, kana ana sa ran za a kafa tsarin ci-gaba da daidaita manufofin ƙasashe mambobin ƙungiyar.
Majiyoyin sun ce taron, wanda ke zama na farko na tuntuɓar juna tsakanin sabuwar gwamnatin Amurka da ƙawayenta na ƙungiyar NATO, zai taɓo batutuwan da suka shafi tsaro da dama, waɗanda suka haɗa da haɗin gwiwa kan tsaro, da yaƙin Ukraine, da kuma haɗin gwiwar NATO da kawayenta a yankin Asiya da tekun Pasific.
Za a gudanar da taron ne cikin rukuni huɗu.
Rukunin farko na taron wanda kasashe mambobin NATO 32 ne kawai za su halarta, zai mai da hankali ne kan raba nauyi, da kuɗaɗen da za a kashe kan tsaro, da kuma tsaron Turai, da ƙarfafa masana’antun samar da kayayyakin tsaro da kuma shirye-shiryen taron ƙolin ƙungiyar NATO da ke tafe a birnin Hague a watan Yuni.
Tattaunawar za ta kuma taɓo yakin Rasha da Ukraine da kuma tasirinsa na dogon lokaci kan tsaron Turai.
Matsayin Turkiyya
Ana sa ran Fidan zai jaddada muhimmancin rawar da Ankara ke takawa wajen tabbatar da tsaron ƙasashen Turai da Atlantic, lura da cewa, Turkiyya ta kasance ginshiki na ɓangaren kuɗu maso gabashin NATO, tare da ba da gudummawarta ga zaman lafiyar yankin ta hanyar ƙarfin soja da kuma ci-gaban masana'antar tsaro.
Rukunin taron na biyu zai faɗaɗa tattaunawar abokan haɗin gwiwar NATO na yankin Asiya-Pacific - da suka haɗa da ƙasar Austiraliya, da Koriya ta Kudu, da Japan, da New Zealand don magance ƙalubalen tsaro da ƙarfafa haɗin gwiwa.
Ana sa ran Fidan zai jaddada batun ƙalubalen tsaro da duniya ke fuskanta tare da buƙatar haɗin gwiwa tsakanin NATO da abokanta na yankin Indiya-Pacific.
Sai kuma rukuni uku na taron, wanda aka ayyana shi a matsayin Majalisar NATO-Ukraine, da zai haɗa da ministan harkokin wajen Ukraine Andrii Sybiha da Babban Wakilin Ƙungiyar EU Kaja Kalas.
Tattaunawar da za gudanar za su mayar da hankali ne kan buƘatun Ukraine kan matakan gaggawa na soja da tattalin arziki, da kuma fa'idar yanayin siyasa na yaƘin da yuwuwar samar da tsarin tsaro bayan yaƘin.
Turkiyya, wacce ta taka muhimmiyar rawa wajen shiga tsakani a tattaunawar da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine, ana sa ran za ta ci gaba da bayar da gudumawa a shawarwarin diflomasiyya.
Kazalika ana sa ran Fidan zai jaddada matsayin Turkiyya, tare da tabbatar da goyon bayanta kan 'yancin kai na Ukraine, da kuma 'yancin yankin yayin da take ba da shawarar tsagaita bude wuta da zaman lafiya mai dorewa a yakin da ke ci gaba da gudana a tsawon sama da shekaru uku.
Sai kuma rukunin ƙarshe na taron da zai mayar da hankali kan haɗin gwiwa tsakanin kungiyar NATO da EU, inda Kalas zai yi wa ministocin ƙungiyar ƙarin haske kan sabbin tsare-tsare na tsaro na ƙungiyar EU da suka haɗa da batun Asusun tsaro na Turai da kuma dabarun yaki.
Haka kuma ana sa ran Fidan zai jaddada Turkiyya a matsayin wani ɓangare na tsaron ƙasashen Turai da ba za a iya tafiya babu ita ba, kuma dole ne ƙoƙarin tsaron EU ya haɗa da ƙawayen Turai da ke wajen ƙungiyar.
Har ila yau ana sa ran zai bayyana matsayin Turkiyya game da shiga cikin ayyukan masana'antun tsaro na EU.
Comments
No comments Yet
Comment