Dollar

38,0114

0.26 %

Euro

41,7905

-0.59 %

Gram Gold

3.775,7500

-0.55 %

Quarter Gold

6.298,5600

-0.1 %

Silver

38,3800

-1.21 %

Gangamin wanda aka yi wa take da Safe2Eat na da nufin wayar da kan masu sayen kayayyaki da bayanai na yau da kullun bisa ga bayanan kimiyya kan abinci

Turkiyya ta shiga gangamin ingancin abinci na EU don wayar da kan masu sayen kayayyaki

Turkiyya ta shiga cikin gangamin Safe2Eat wanda Hukumar Kula da Abinci ta Tarayyar Turai ta ƙaddamar don taimaka wa masu sayen kayayyakin abinci samun ingantattun bayanan yin zaɓi kan abinci.

A cewar wata sanarwa da Ma'aikatar Noma ta Turkiyya ta fitar a ranar Laraba, sashen sadarwa na gangamin wanda a shekarun baya an buɗe shi ne kawai ga ƙasashe mambobin ƙungiyar Tarayyar Turai, wanda kuma a wannan shekara ƙasashen da suka nemi shiga suka samu dama, na da nufin wayar da kan masu sayen kayayyaki da bayanai na yau da kullum bisa ga bayanan kimiyya kan abinci.

Tun dai daga shekarar 2020, gangamin ya ƙuduri aniyyar tabbatar da cewa masu sayen kayayyaki sun yi zaɓin da ya dace tare da hana ɓarnar abinci.

Ƙarƙashin gangamin na Safe2Eat, wanda ya kai ga sama da kashi 45 cikin ɗari na mutanen da aka yi niyya isa gare su a fadin Turai a bara, ya wayar da kan mutane sama da miliyan 50 a Turai kan ingancin abinci ta hanyar saƙonnin da aka wallafa ta kafofin sada zumunta da sauran hanyoyin sadarwa.

Gangamin ya sanya masu sayen kayayyaki sauya ɗabi’unsu zuwa ba da “fifiko kan ingancin abinci’’ a yayin yin zaɓin da ya shafi abinci.


Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#