Sport
Dollar
38,1034
0.22 %Euro
43,6370
-0.09 %Gram Gold
4.072,6200
0.23 %Quarter Gold
6.720,2300
0 %Silver
39,8800
0.27 %Tsohon Shugaban na Nijeriya Muhammadu Buhari ya bayar da misali da shi kansa, irin yadda ya bar ofis ba tare da ya mallaki ko da kadara daya a kari a kan abin da yake da shi kafin ya zama shugaban kasa ba.
Tsohon Shuguban Nijeriya Muhammadu Buhari ya shawarci gwamnonin jam’iyyar APC su ringa aiwatar da tsare-tsaren da za su amfani jama’a.
Buhari yana magana da gwamnonin ne lokacin da suka kai masa ziyarar sallah a gidansa a Kaduna, kamar yadda wata sanarwa da Malam Garba Shehu ya fitar a ranar Laraba.
Sanarwar ta ambato tsohon shugaban yana bayyana gamsuwa da irin yadda gwamnonin na APC ke tafiyar da al’amuransu, sannan ya yi kira a gare su da su kara zange dantse wajen ci-gaban kasa.
“Ya kamata shugabanni su mayar da hankali kan jin dadin jama’a, ba wai jin dadin kansu ba,” a cewar sanarwar.
Buhari ya kuma bayar da misali da shi kansa irin yadda ya bar ofis ba tare da ya mallaki ko da kadara daya kari a kan abin da yake da shi kafin ya zama shugaban kasa ba.
Ya kuma gode wa Shugaba mai ci, Bola Tinubu saboda yadda ya gyara masa gidansa na Kaduna, yana mai cewa “duk da fasalin gidan bai sauya ba daga waje, amma an gyara shi sosai daga ciki.”
Da yake magana a madadin gwamnonin, Shugaban Kungiyar ta gwamnonin APC, wanda kuma shi ne gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma, ya ce tarihin Nijeriya ba zai taba mantawa da Buhari ba, saboda irin yadda ya bai wa dimokuradiyya gudunmawa.
Comments
No comments Yet
Comment