Sport
Dollar
38,4292
0.2 %Euro
43,8350
-0.02 %Gram Gold
4.095,0600
-0.84 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Da yawa daga cikin shugabannin kasashe fiye da 50 da suka halarci jana'izar sun riga sun shiga cikin Basilica don gabatar da gaisuwa ga gawar Fafaroma, wanda ya rasu ranar Litinin yana da shekaru 88 a duniya.
Dubun dubatar masu zaman makoki da shugabannin ƙasashen duniya ciki har da shugaban kasar Amurka Donald Trump ne suka cika dandalin St Peter a yau Asabar domin jana'izar Fafaroma Francis, mai rajin kare haƙƙin talakawa kuma shugaban Cocin Katolika wanda shi ne na farko da ya fito daga yankin Latin Amurka.
Wasu sun shafe dare don samun kujera don bikin, inda 'yan sanda suka ba da rahoton mutane kusan 150,000 sun hallara a dandalin da titunan da ke kewaye tun kafin a fara jana’izar da karfe 10:00 na safe (0900 GMT).
Jama'a sun yi ta shewa yayin da aka fito da akwatin gawar Fafaroma daga Cocin St Peter zuwa cikin dandalin.
Da yawa daga cikin shugabannin kasashe fiye da 50 da suka halarci jana'izar sun riga sun shiga cikin Basilica don gabatar da gaisuwa ga gawar Fafaroma, wanda ya rasu ranar Litinin yana da shekaru 88 a duniya.
Baƙin sun hada da shugaban kasar Argentina Javier Milei da Yarima William na Birtaniya da kuma Volodymyr Zelensky na Ukraine -- wadanda suka gana da Trump a gefe, a cewar mai magana da yawun Ukraine.
Francis ya yi ƙoƙarin kawo sauye-sauye a tsarin yadda ake gudanar da cocin tsawon shekaru 12 da ya shafe yana jagorancinta, kuma mutuwarsa ta ja hankalin duniya baki ɗaya.
Comments
No comments Yet
Comment