Sport
Dollar
38,2612
0.13 %Euro
43,8713
-0.48 %Gram Gold
4.214,3700
0.12 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%A wasiyyarsa, Francis ya bayyana inda yake so a binne shi, tare da zanen yadda yake so a binne shi.
Fafaroma Francis ya bayyana abin da yake so a yi bayan mutuwarsa a wasiyyarsa, inda ya nemi a binne shi a wani kabari mara ado, a cocin da yake so a Roma, Santa Maria Maggiore.
"Yayin da nake jin cewa rayuwata a duniya ta kusa zo ƙarshe kuma tare da karsashin fatan Rayuwa Madawwamiya, ina son in bayyana wasiyyata game da inda za a binne ni ne kawai," kamar yadda Fafaroma ya bayyana a wasiyyarsa da ya rubuta ranar 29 ga watan Yuni, ta shekarar, 2022, da fadar Vatikan ta wallafa ranar Litinin.
"Ina neman a binne gawata domin ta jira tashin ƙiyama a cocin Fafaroma na Santa Maria Maggiore," in ji Fafaroman, wanda ya yi ta neman ziyartar muhimmin wurin mai tsarki na Katolikan kafin da kuma bayan ko wace tafiyar da ya yi a matsayinsa na Fafaroma.
A wasiyyarsa, Francis ya bayyana daidai wurin da yake so a binne shi tare da bada wani zane domin bayyana yadda yake so a binne shi, kuma ya ce an riga an ƙayyade kuɗin da za a kashe wajen binne shi.
"Dole kabarin ya kasance a doron ƙasa na duniyar Earth, gaya, ba tare da wani ado ba kuma ya kasance da rubutun da ke cewa: Franciscus."
A ƙarshen wasiyyarsa, jagoran addinin ‘yan Ɗrikar Katolika na Duniya ya nemi Allah ya "ya bada ladan da ya kamaci waɗanda suke so na kuma za su ci gaba da yi mini addu’a ".
"Na ba da wahalar da na sha a ƙarshen rayuwata ga Allah domin zaman lafiyar duniya da kuma ‘yanuwantaka tsakanin mutane."
Comments
No comments Yet
Comment