Sport
Dollar
38,4232
0.21 %Euro
43,7024
-0.17 %Gram Gold
4.052,7000
-1.86 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Masu ƙoƙarin lalata alaƙar Turkiyya da duniyar Turkawa ba za su yi nasara ba, in ji Ministan Harkokin Wajen Turkiyya.
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya yi gargaɗin cewa duk wani ƙoƙari na raunana alaƙar Turkiyya da ƙasashen duniyar Turkawa ba zaai yi nasara ba.
Da yake jawabi a ranar Alhamis a yayin taron manema labarai na haɗin gwiwa da takwaransa na Norway, Espen Barth Eide a Ankara, Fidan ya ce “Ƙutungwilar waɗanda ke son kawo matsala tsakanin mu da duniyar Turkawa ba za ta yi nasara ba.”
“Duniyar Turkawa gaba ɗaya za ta ci gaba da tsaya wa tare da Turkawan Cyprus” in ji shi, yana mai ƙarawa da cewa “Za mu ci gaba cikin haƙuri da ɗabbaka manufofinmu kan wannan batu.”
Kan batun Gaza, Fidan ya ce an ɗauki kusan kwanaki 50 ba a bayar da dama a kai kayan taimako Gaza ba, yana mai cewa bai kamata a yi amfani da yunwa a matsayin makami ba wajen azabtar da wasu mutanen.
A nasa ɓangaren, Espen Barth Eide ya bayyana damuwa bisa “shiru” kan Gaza, yana gargaɗin cewa ƙasashen Yamma da yawa na yin kuskuren ƙin ɗaukar tsayayyiyar matsaya.
Shekaru 100 na alaƙar diflomasiyya
Fidan ya kuma sanar da cewa 2026 za ta zama shekara ta 100 da kulla alaƙar diflomasiyya tsakanin Turkiyya da Norway, inda ya bayyana babbar aniya ta zurfafa alaƙar ɓangarorin biyu.
Da yake bayani kan haɓaka haɗin kai, ministan ya yi tsokaci kan cewa kasuwancin da ke tsakaninsu ya haura na dala biliyan ɗaya, kuma ƙasashen biyu na “aiki sosai” don ƙara adadin.
Sufurin teku ya zama babban jigon haɗin kan tattalin arziki, inda ake samar da jiragen ruwan Turkiyya da dama a kamfanonin Norway.
Ministan ya kuma yi ƙarin haske kan haɓakar haɗin kai a bangaren masana’antar tsaro inda ya ƙarfafi gwiwar kamfanonin ɓangarorin biyu da a yi sababbin haɗin kai.
Ya jaddada muhimmancin ɓangaren makamashi da ba a amfana da shi, tare da jaddada bukatar Turkiyya ga Norway ta goya mata baya wajen yaƙi da ‘yan ta’addar PKK da FETO.
Comments
No comments Yet
Comment