Dollar

38,4259

0.22 %

Euro

43,6809

-0.26 %

Gram Gold

4.071,5600

-1.41 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Shugaban Turkiyya ya bayyana matsayin kasar kan harkokin wasanni a duniya yayin bikin da ke da alaka da shirin EURO 2032.

A shirye Turkiyya take ta karbi gasar Olympics a lokacin da EUFA ta bude ofis a Istanbul —  Erdogan

Shugaban Turkiyya ya bayyana cewa ƙasar tana da isasshen ƙarfin da za ta iya ɗaukar nauyin shirya dukkan nau'ikan wasannin ƙasa da ƙasa, har ma da gasar Olympics.

An ba da wannan tabbacin ne saboda ayyuka da shirye-shiryen “da muka kawo ƙasarmu cikin shekaru 23 da suka gabata,” in ji Recep Tayyip Erdogan a ranar Alhamis yayin bikin buɗe ofishin UEFA a Istanbul.

“Mun ɗaukaka Turkiyya zuwa wani mataki daban a fannin saka hannun jari a wasanni. Mun buɗe sababbin wuraren wasanni bisa ga bukatun jihohinmu.

“Mun ƙara adadin wuraren wasanni daga 1,575 zuwa 4,470,” in ji shi. Ya jaddada cewa an magance matsalolin da ƙasar ke fuskanta a fannin kayan aikin wasanni.

Erdogan ya bayyana cewa UEFA ta buɗe ofishin wakilci a Turkiyya a karon farko bayan London da Brussels, kuma ta wannan ofishin, ƙasar za ta ƙara kusanci da UEFA don ci-gaban ƙwallon ƙafa na Turkiyya da kuma gudanar da ayyuka tare.

Ya ƙara da cewa ofishin wakilcin zai taimaka wajen saurin sadarwa da haɗin kai tsakanin UEFA da ƙungiyoyin yankin. “Ina ganin wannan ofishin zai taka muhimmiyar rawa a shirye-shiryen wasannin ƙwallon ƙafa da za mu karɓa nan gaba,” in ji shi.

Bayan bikin buɗe ofishin, Erdogan ya karɓi shugaban UEFA Aleksander Ceferin. Ministan Matasa da Wasanni na Türkiye Osman Askin Bak da mai ba da shawara kan harkokin waje da tsaro Akif Cagatay Kilic suma sun halarta.

Ofishin UEFA a Istanbul zai taka muhimmiyar rawa wajen tsara gasar ƙarshe ta UEFA Europa League a 2026, gasar ƙarshe ta UEFA Conference League a 2027, da kuma gasar ƙwallon ƙafa ta Turai ta UEFA 2032 (EURO 2032) da za a shirya tare da haɗin gwiwar Turkiyya da Italiya.

Shugaba Erdogan ya tunatar da mahalarta game da nasarar Turkiyya wajen karɓar baƙuncin wasu wasannin ƙarshe na UEFA a shekarun baya. Waɗannan sun haɗa da gasar ƙarshe ta UEFA Champions League ta 2005 tsakanin Liverpool da AC Milan, wadda aka fi sani da ɗaya daga cikin mafi ban sha'awa a tarihin ƙwallon ƙafa, da gasar ƙarshe ta UEFA Cup ta 2009, da UEFA Super Cup ta 2019, da gasar ƙarshe ta UEFA Champions League ta 2023.

Shugaban UEFA Aleksander Ceferin ya halarci buɗe sabon ofishin UEFA a Istanbul, inda ya kira wannan matakin a matsayin dabarar tabbatar da gudanar da manyan gasar ƙwallon ƙafa masu zuwa ba tare da wata matsala ba.

“Duba da yawan manyan abubuwan da ke tafe, mun yanke shawarar buɗe ofishi a nan Istanbul don mu kasance muna da ƙarfi a cikin gida da tabbatar da gudanar da waɗannan gasar masu daraja cikin nasara,” in ji Ceferin a lokacin bikin buɗe ofishin.

Ya yaba da ƙoƙarin Turkiyya wajen shirya manyan gasar ƙwallon ƙafa, ciki har da gasar ƙarshe ta UEFA Champions League a 2005 da 2023, da gasar ƙarshe ta UEFA Cup a 2009, da UEFA Super Cup a 2019.

Ceferin ya ce ƙasar tana nuna ƙwazo da himma wajen zama ɗaya daga cikin manyan masu karɓar baƙuncin wasanni a duniya.

“An ɗaga martabar inganci sosai. UEFA tana goyon bayanku gaba ɗaya a wannan tafiya. Duba da yawan abubuwan da ke tafe, mun yanke shawarar buɗe ofishi a nan Istanbul don tabbatar da gudanar da waɗannan gasar cikin nasara,” in ji shi.

Ceferin ya nuna tabbacinsa kan haɗin gwiwar UEFA da hukumomin Turkiyya, yana cewa, “Kasancewarmu tare, ba kawai za mu cika abubuwan da ake tsammani ba ne — za mu zarce su. Za mu sanya ma'auni don gasar a nan gaba.”

“A yanzu, muna kawo dukkan ƙwarewarmu da dabarunmu don tabbatar da cewa waɗannan abubuwan sun zama na musamman,” in ji shi. Ya kuma gode wa Erdogan da gwamnatin Turkiyya, da Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Turkiyya saboda goyon bayan da suke bayarwa.

“Muna sa ran gudanar da gasar ban mamaki. Ina sa ran a buga wasan ƙarshe a gasar EURO 2032 tsakanin Turkiyya da Italiya,” in ji shi.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#