Dollar

38,1216

0.1 %

Euro

43,6148

1.3 %

Gram Gold

4.051,2600

2.43 %

Quarter Gold

6.511,6500

0 %

Silver

40,3700

1.95 %

"Ina da matuƙar, matuƙar kyakkyawar alaƙa da Turkiyya da shugabanta," a cewar Shugaba Trump a cikin wannan makon.

Trump yana duba yiwuwar ziyarar Turkiyya a yayin ziyarar Gabas ta Tsakiya

Shugaban Amurka Donald Trump yana duba yiwuwar sanya Turkiyya a cikin jadawalin ƙasashen da zai je a ziyarar da zai kai yankin Gabas ta Tsakiya a watan gobe, kamar yadda CNN Arabic ta rawaito.

Mai yiyuwa ziyarar ta biyo bayan tsayawar da zai yi a Saudiyya da Qatar da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, kamar yadda wani babban jami'in Fadar White House da wasu mutane biyu da suke da masaniya kan shirin tafiyar, waɗanda suka yi magana da CNN a ranar Alhamis.

Majiyoyi sun ce, ba a yanke shawara ta ƙarshe ba tukuna, kuma ana ci gaba da shirye-shirye.

Kyakkyawar alaƙa da Turkiyya

Wani babban jami'in Fadar White House ya bayyana cewa Trump ya tattauna batun wannan ziyara yayin wata tattaunawa ta waya da shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a baya bayan nan.

Majiyoyi sun kuma bayyana cewa Trump ba shi da niyyar ziyartar Isra'ila yayin wannan tafiya.

Fadar White House ba ta mayar da martani ba har yanzu kan buƙatar jin ƙarin bayani da kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya yi ba.

Trump ya taɓa bayyana kalamai masu kyau game da dangantakarsa da Erdogan.

“Ina da kyakkyawar dangantaka sosai da Turkiyya da shugabanta,” in ji Trump a farkon wannan mako, yayin da yake tare da Firayiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a Fadar White House.

Trump ya bayyana Erdogan a matsayin “jajirtaccen mutum, mai basira sosai, wanda ya yi abin da ba wanda ya taɓa yi,” yana nuni da maganganun da ya yi cewa yana ganin “Turkiyya ce ta taka muhimmiyar rawa wajen kifar da tsohon Shugaban Siriya Bashar al-Assad.”

Idan aka yi wannan ziyara, za ta kasance ziyarar farko da Trump zai kai Turkiyya a matsayin shugaban ƙasa.

Waɗanda suka gabace shi, George W. Bush ya kai ziyarar a 2004, Barack Obama kuma ya ziyarci Turkiyya sau biyu a 2009 da 2015.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#