Sport
Dollar
38,0136
0.26 %Euro
42,1456
0.21 %Gram Gold
3.801,0000
0.11 %Quarter Gold
6.304,8300
0 %Silver
38,8900
0.08 %Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya buƙaci takwaransa na Jihar Edo Monday Okpebholo ya fito da mutanen da suka kashe mafarauta 16 sannan a nuna wa duniya su don kowa ya gan su.
Gwamnan Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya Abba Kabir Yusuf ya buƙaci takwaransa na Jihar Edo, Monday Okpebholo da ya biya diyyar mafarauta 16 da aka kashe a jiharsa a kan hanyarsu ta komawa gida domin bukuwan Sallah.
Gwamna Abba ya yi kiran ne ranar Litinin a gidan gwamnatin Kano lokacin da takwaransa na Jihar Edo Monday Okpebholo da tawagarsa suka kai masa ziyarar jaje ga gwamnatin Kano da al'ummar jihar kan kisan da masu mutanen ƙauyen Uromi na ƙaramar hukumar Esan suka yi wa matafiyan a makon jiya.
Wata sanarwa da Sanusi Bature Dawakin Tofa, mai magana da yawun Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fitar ta ambato gwamnan yana kira da a nuna wa duniya fuskokin mutanen da suka yi wannan ɗanyen aiki bayan kamun da aka yi musu.
“Mun ji daɗin yadda aka yi gaggawar ɗaukar mataki kawo yanzu, amma dole ne a yi hukunci kamar yadda ya kamata. Ya dace al’ummar Jihar Kano, da ma duka ‘yan Nijeriya su ga an hukunta mutanen da suka yi wannan kisa a bainar jama’a,” in ji Gwamna Abba.
Ya ƙara da cewa, “Muna so a tabbatar da biyan diyya ga iyalansa waɗanda aka kashe. Na san kai mutum ne na gari da ke faɗa ya cika, kamar yadda ka ce za a biya diyya, muna so a biya diyya cikakkiya, kuma a kan lokaci."
A jawabinsa, Gwamna Okpebholo ya nuna matuƙar takaicinsa game da kisan da aka yi wsa matafiya ‘yan Jihar Kano a jiharsa, yana mai cewa kawo yanzu an kama mutum 14 da ake zargi suna da hannu a lamarin kuma za a hukunta su.
Comments
No comments Yet
Comment