Dollar

38,0134

0.27 %

Euro

41,8767

-0.39 %

Gram Gold

3.769,5700

-0.72 %

Quarter Gold

6.321,1900

0.26 %

Silver

37,5900

-3.26 %

Dangane da hare-haren da Isra'ila ta kai a lokaci guda ta sama da ta kasa a wurare da dama a Siriya a ranar Laraba, Ankara ta ce babu wata tsokana ko barazana daga bangaren Siriya.

Turkiyya ta yi Allah-wadai da "mamaya da cin zali" na Isra'ila da kalaman tsokana na ministocinta

Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta yi kakkausar suka kan kalaman da ministocin Isra'ila suka yi a baya bayan nan, tana mai cewa kalaman na tsokana ne da kuma nuni da manufofin Isra'ila na "cin zali da mamaya”.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a yammacin ranar Alhamis, ma'aikatar ta soki gwamnatin Isra'ila, inda ta zarge ta da rura wutar rikicin yankin.

Ma'aikatar ta yi tambaya kan dalilin da ya sa Isra'ila ta damu da abubuwan da ke faruwa a Siriya da Lebanon, wanda ta bayyana a matsayin wani kyakkyawan fata na samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Ta kuma jaddada cewa, wadannan ci gaban na samun goyon bayan kasashen duniya da dama, don haka bai kamata a rika kallonsu a matsayin barazana ba.

Martanin na Turkiyya ya zo ne a matsayin martani ga kalaman Ministan Harkokin Wajen Isra'ila Gideon Saar game da kasancewar Turkiyya a Siriya da Labanon, da sauran yankuna.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#