Dollar

38,0149

0.26 %

Euro

42,1345

0.2 %

Gram Gold

3.802,9300

0.16 %

Quarter Gold

6.304,8300

0 %

Silver

38,9100

0.15 %

Daga cikin sabbin alƙaluman da aka samu na mutanen da suka kamu da cutar, sama da ma’aikatan lafiya 20 ne suka kamu da cutar zazzabin Lassa a jihohi takwas daga cikin 33 na ƙasar

Mutane 118 sun mutu sakamakon zazzaɓin Lassa a Nijeriya - NCDC

Zazzaɓin Lassa ya kashe mutane 118 a Nijeriya a cikin watanni uku na farkon shekarar 2025, a cewar Cibiyar Yaƙi da Cututtuka masu yaɗuwa ta ƙasar (NCDC).

Haka kuma NCDC ta ce an samu mutane 3,465 da ake zargin sun kamu da cutar a faɗin ƙananan hukumomi 91 a jihohi 33 na kasar a shekarar 2025.

Cutar wadda ɓeraye ke ɗauke da ita kana aka fara gano ta a shekarar 1969 a jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar, ta kashe dubban mutane a tsawon shekaru, musamman a yankunan karkara, saboda rashin kula da tsaftar abinci.

Duk da cewa an shafe shekaru ana neman rigakafin cutar, ba a samun wani gagarumin ci-gaba a tsaftar muhalli da zai hana ɓeraye shiga gidaje da ake ajiye abinci da kayan aiki ba.

 Hanyoyin da ba su dace ba

A tsakanin watan Janairu zuwa Maris na 2025, NCDC ta tabbatar da cewa adadin mutanen da suka kamu da cutar zazzaɓin Lassa ya kai 645, inda mutane 118 daga cikinsu suka mutu, adadin da ya kai kashi 18.3 cikin ɗari, a cewar Daraktan Hukumar NCDC Jide Idris a wata sanarwa da ya bayyana a ranar Litinin.

An yi ta samun mutuwar mutane kusan 100 ko fiye da haka a Nijeriya sakamakon zazzaɓin Lassa a kowanne watanni huɗu na shekara a kwanan nan.

Daga cikin sabbin alƙaluman da aka samu na mutanen da suka kamu da cutar, sama da ma’aikatan lafiya 20 ne suka kamu da cutar zazzabin Lassa a jihohi takwas daga cikin 33 na ƙasar, in jide Idris.

Ya ce cibiyoyin kiwon lafiya na fama da ƙarancin ma’aikata yayin da majinyata da dama ke jinkirta neman magani, inda suka gwammance su yi wa kansu magani tare da bin sauran hanyoyin da ba su dace ba, waɗanda galibi ba su da inganci.

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#