Sport
Dollar
38,1137
0.18 %Euro
42,0543
-0.85 %Gram Gold
3.708,4600
-2.33 %Quarter Gold
6.293,2300
-0.18 %Silver
36,1600
-6.93 %Ranar Juma’ar, a rana ta ƙarshe a zaman hukumar kare haƙƙin dan’adam ta MDD na 58, an ƙada kuri’ar amincewa ga Albanese ta yi wa’adi na biyu mai shekara uku, lamarin da ya tsawaita aikinta zuwa shekarar 2028.
Hukumar Kare Haƙƙin dan’adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya MDD ta tsawaita wa’adin aikin Francesca Albanese a matsayin wakiliya ta musamman kan ƙasar Falasɗinawa da aka mamaye da ƙarin shekara uku, duk da adawa daga ƙungiyoyi magoya bayan Isra’ila, ciki har da Amurka.
Ranar Juma’a, a ranar ta ƙarshe ta zaman hukumar kare haƙƙin dan’adam ta MDD na 58, an ƙada kuri’ar amincewa da wa’adi na biyu mai shekara uku wa Albanese, lamarin da ya tsawaita wa’adin aikinta zuwa shekarar 2028.
Ta kasance tana fuskantar ƙarin matsin lamba daga ƙungiyoyi masu goyon bayan Isra’ila da ‘yan siyasa da ke neman kawo ƙarshen wa’adin aikinta.
Wasu ƙasashe sun nuna shakku wajen goyan bayan sake ba ta aikin domin yadda take sukar Isra’ila a bayyane.
Albanese ta kasance akai-akai mai bayyana abin ta kira kisa kiyashi da kisan ƙare dangi da ake yi kan Falasɗinawa a rahotannin da ke take bayarwa a hukumance da hirarrakin da take a kafafen watsa labarai.
Ƙungiyoyi masu goyon bayan Isra’ila
Sukar da ake yi wa Albanese ta samu goyon bayan mutane irin su ɗan majalisar Birtaniya na jam’iyyar Labour David Taylor, wanda ya zarge ta da bayyana harin Hamas na ranar 7 ga watan Oktoba a matsayin wani harin da ya dace tare da bayyana Isra’ila a “matsayin mamayar ‘yan kama wuri zaune” a wata hira da kafar The Jewish Chronicle, wata jarida mai goyon bayan Isra’ila.
Ƙungiyoyi masu goyon bayan Isra’ila, ciki har da UN Watch, sun kasance a gaba-gaba wajen sukarta.
UN Watch ta wallafa rahoto mai shafi sama da 60 tana mai sukar Albanese da zargin ƙin jinin Yahudawa da kuma “ta’addanci” a ƙarƙshin aikinta na MDD. Ƙungiyar ta kuma ƙaddamar da takardar ƙara inda take neman hukumar kare hakkin dan’adam ta MDD (UNHRC ) ta yi watsi da sake ba ta aikin.
A wani zaman hukumar UNHRC kwanan nan a Geneva, daraktan UN Watch Hillel Neuer ya nemi a kori Albanese nan take.
Sauran ƙungiyoyi, ciki har da ƙungiyar Yahudawa ta Duniya (World Jewish Congress) da kuma ƙungiyar matasa masu kaifin kishin kafa ƙasar Isra’ila the Zionist youth organisation Betar, sun soki Albanese.
An yi iƙirarin cewa Betar ta yi barazanar kai mata hari yayin wata ziyara da ta kai Landan, inda aka yi ishara da hare-haren saman da Isra’ila ta kai Lebanon bara.
Comments
No comments Yet
Comment