Sport
Dollar
37,9905
0.12 %Euro
42,2959
0.26 %Gram Gold
3.774,6500
-0.58 %Quarter Gold
6.304,8300
0 %Silver
38,4900
-0.95 %Donald Trump ya sanar da sanya haraji na kashi 34 kan dukkan kayayyakin da za a shiga ƙasar da su daga China, sai kuma kashi 20 daga kayayyakin Tarayyar Turai — biyu daga cikin manyan abokan kasuwancin Amurka.
Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da sanya jerin sabbin haraji kan ƙasashen duniya a jawabinsa na 'Ranar 'Yanci' matakin da ake gani zai ta’azzara yaƙin harkokin cinikayya a duniya.
Ya sanar da wannan mataki ne ranar Laraba, yana mai cewa sauran ƙasashe "sun daɗe ana cutar ƙasarmu da kwashe arzikinta".
Trump ya riƙe wani allo a yayin da yake jawabi, inda ya nuna daga yanzu Amurka za ta karɓi harajin da ya kai kashi 34 kan kayan da aka shigar ƙasar daga China, sai kashi 20 daga kayan da aka shigar Amurka daga Tarayyar Turai, kashi 25 daga Koriya ta Kudu, kashi 24 daga Japan, kashi 32 daga Taiwan, kashi 29 daga Pakistan da kashi 10 daga Turkiyya.
"Wannan ba cikakken mayar da martani ba ne," in ji Trump. "Wannan martani ne na adalci."
"A kwashe shekaru fiye da 50 an damfarar masu biyan haraji na Amurka," a cewar Trump a jawabin da ya yi a Fadar White House. "Amma hakan ba zai sake faruwa ba."
"Hakan samun ‘yancin kanmu ne a harkokin kasuwanci," in ji Trump a yayin da yake sanar da sanya jerin harajin. "An kwashe shekaru aru-aru ana tilasta wa Amurka masu aiki tuƙuru zama ‘yan kallo a yayin da sauran ƙasashe suke ci gaba da samun arziki da ƙarfi, mu kuma an bar mu a baya. Amma yanzu lokaci ne da za mu samu ci gaba
“A lokuta da dama, masoyinka ya fi maƙiyinka illa a harkokin cinikayya," a cewar Trump.
"Mun sauƙaƙa wa ƙasashe da dama kuma hakan ya sa kasuwancinsu yana tafiya ba tare da matsala ba," in ji Trump da yake magana a kan abokan harkokin kasuwancin Amurka, musamman Mexico da Canada. "Me ya sa muke yin hakan? Ina nufin, a wane lokaci ya kamata mu gaya musu su je su kula da harkokinsu."
Comments
No comments Yet
Comment