Dollar

37,9676

-0.02 %

Euro

41,5961

0.56 %

Gram Gold

3.845,2500

0.48 %

Quarter Gold

6.332,2600

0 %

Silver

40,8900

-1.32 %

Wani babban mai ba da shawara ga Jagoran Addinin na Iran ya yi gargaɗin cewa harin Amurka zai sa Iran ta zama ba ta da wani zaɓi face samar da makaman nukiliya don tsaro.

Kai wa Iran hari zai sa ta 'rasa wani zaɓi' in ba samar da nukiliya ba

Iran za ta zama ba ta da zaɓi in ba mallakar makaman nukiliya ba idan har Amurka ko ƙawayenta suka kai mata hari, a cewar wani babban mai bai da shawara ga Jagoran Addini na Kasar Ali Khamenei

“Ayanzu ba ma samar da makaman nukiliya, amma idan kuka yi kuskure kan batun nukiliya, za ku tilasta wa Iran ta fara aikin samar da shi, saboda dole ne da ta kare kanta,” kamar yadda Ali Larjani ya shaida wa gidan talabijin ɗin ƙasar a ranar Litinin.

“Iran ba ta son haka, amma idan kuka matsa lamba...zai zama ba ta da zaɓi,” a cewarsa.

Kalaman nasa sun zo ne bayan Shugaban Amurka Doland Trump ya yi wa Iran barazana ranar Lahadi, da cewa za a yi mata ruwan bama-bamai idan ba ta amince da ta tattauna da Amurka ba kan shirinta na nukiliya, abin da ya sa ya zama gargadin amfani da karfin soja da ya fi fitowa ƙarara tun da ya karɓi mulki.

“Idan ba su cim ma yarjejeniya ba, za a jefa masu bama-bamai. Zai zama ruwan bama-bamai irin wanda ba su taba gani ba,” a cewar Trump yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na NBC News.

A martaninsa na farko ga Trump, Khamenei ya yi gargadin cewa dak wani “hari daga waje” zai fuskanci “mummunan mayar da martani.”

Larjani ya ce Amurka za ta tilasta wa Iran ta ɗauki mataki “daban” idan ta zaɓi ta jefa wa Iran bamabamai da kanta ko ta hanyar amfani da Isra’ila.

“Iran ba ta son bin wannan hanyar, amma idan kuka matsa lamba, to ta samu dalili kuma zai zama ba ta da wani zaɓin daban. Mutane za su tura mu bango mu ɗauki mataki, domin dole ne tsaron kasa,” kamar yadda ya bayyana.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#