Sport
Dollar
38,2896
0.06 %Euro
43,7745
0.11 %Gram Gold
4.151,2400
-0.23 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Mayaƙan Boko Haram da ISWAP sun mayar da hankali ne kan arewa maso gabashin Nijeriya kuma suna kai hare-hare kan dakarun tsaro da fararen-hula, inda suka kashe dubban mutane ko kuma raba su da gidajensu.
Ƙungiyar ta’addanci ta ISWAP ta ɗauki alhakin kai hare-hare kan dakarun tsaron Nijeriya tare da fararen-hula a arewa maso gabashin Nijeriya a farkon watan Afrilu.
A saƙonni bakwai da ta wallafa a kafarta ta "Amaq," ISWAP ta yi iƙirarin cewa ita ta ƙaddamar da hare-haren, inda ta kafa hujja da hotuna da bidiyon da ke nuna ɗaya daga cikin hare-hare.
Hare-haren da ta kai a jihar Borno ta ƙaddamar da su ne kan barikin sojin na garin Yamtage, inda ta yi iƙirarin cewa ta kashe sojoji uku tare da ƙona barikin.
ISWAP ta kuma yi iƙirarin cewa mayaƙanta sun kama tare da kashe ‘yan sa-kai huɗu da ke mara wa sojin Nijeriya baya.
A jihar Adamawa, ƙungiyar ta ɗauki alƙain kai hare –hare biyu a ƙauyen Banga, wadda mutanenta Kiristoci ne.
Harin na farko, wadda aka kai ranar 15 ga watan Afrilu, ya kashe mutane biyu tare da ƙona gidaje 30, kuma Amaaq ta wallafa hotunan harin.
Hari na biyu kan Banga, ranar 16 ga watan Afrilu, ya mayar da hankali ne kan ‘yan sanda masu sintiri a ƙauyen, inda ya lalata wata mota tare da ji ma wasu jami’an ‘yan sanda rauni.
Kafar kuma ta wallafa wasu hotuna da suka nuna yadda aka kai hari a ƙauyen Lareh a jihar Adamawa, tana mai nuna yadda aka ƙona gidaje da kuma wani coci, sai dai wannan bai zo da iƙirarin daukar alhaki ba.
Mayaƙan Boko Haram da ISWAP sun mayar da hankali ne kan arewa maso gabashin Nijeriya kuma suna kai hare-hare kan dakarun tsaro da fararen-hula, inda suka kashe dubban mutane ko kuma raba su da gidajensu.
Gwamnatin Nijeriya ta ce za ta “murƙushe” ƙungiyoyin, kuma ta ƙara kasafin kuɗin tsaro da kashi 40 cikin 100 a shekarar 2025.
Comments
No comments Yet
Comment