Dollar

35,4431

0.27 %

Euro

36,3540

-0.47 %

Gram Gold

3.063,1500

1.01 %

Quarter Gold

4.997,4300

-0.04 %

Silver

34,5800

1.03 %

Continents

Categories

Jam'iyyar Deby wato Patriotic Salvation Movement, ta samu kujeru 124 cikin 188 a majalisar dokokin ƙasar, kamar yadda hukumar zaɓen ƙasar ta bayyana.

Jam'iyya mai mulki a Chadi ta lashe biyu bisa uku na kujerun majalisar dokokin ƙasar

Jam'iyya mai mulki a Chadi ta lashe kashi biyu bisa uku na kujerun majalisar dokokin kasar a zaɓen da 'yan adawa da dama suka kaurace wa a watan da ya gabata, kamar yadda sakamakon zaɓen ya nuna a ranar Lahadi, lamarin da ya ƙara ƙarfin Shugaba Mahamat Idriss Deby kan karagar mulki.

Sakamakon zaben da aka yi a ranar 29 ga Disambar 2024, ya sanya kasar Afirka ta tsakiya mai arzikin man fetur, ta zama cikakkiyar ƙasa mai mulkin dimokuradiya bayan shekara uku da Deby ya karɓi mulki bayan rasuwar mahaifinsa wato Idriss Deby Itno.

Jam'iyyar Deby wato Patriotic Salvation Movement, ta samu kujeru 124 cikin 188 a majalisar dokokin ƙasar, kamar yadda hukumar zaɓen ƙasar ta bayyana.

Kaso 51.56 cikin 100 na masu zaɓe a ƙasar ne suka fita kaɗa ƙuri'a a ƙasar

'Yan adawa sun yi zargin 'rashin gaskiya' a zaɓen

Zaɓen wanda ya haɗa da na yankuna da manyan birane shi ne na farko a Chadi a fiye da shekara 10.

Sai dai jagoran 'yan adawa Success Masra da Jam'iyyarsa ta Transformateurs da wasu da dama sun ƙaurace wa zaɓen, inda suka ce zaɓen ya rasa alƙibla sannan akwai rashin gaskiya a cikinsa. Sai dai gwamnatin ta Chadi ta musanta zargin.

An zaɓi Deby a matsayin shugaban kasa a wani zaɓe mai cike da taƙaddama a watan Mayun 2024, shekaru uku bayan ya ayyana kansa a matsayin shugaban rikon kwarya lokacin da 'yan tawaye suka kashe mahaifinsa a fagen daga.

Tun bayan da Deby ya ci zaɓe, Chadi - wadda muhimmiyar ƙawa ce ga ƙasashen Yamma a yaƙi da ta'addanci a yankin Sahel - ta kawo ƙarshen yarjejeniyar da take da ita da Faransa da kuma yin barazanar janye dakarunta daga ƙungiyar haɗaka ta sojojin da ke yaƙi da ta'addanci a Sahel.

Daƙile hari kan fadar shugaban Chadi

Yanke hulɗar soji da Faransa ta yi ya zo daidai da matakin da kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso suka ɗauka, wanda duka suka fatattaki sojojin Faransa tare da kara ƙulla alaƙa da Rasha.

A makon da ya gabata, jami'an tsaron Chadi sun daƙile wani hari da aka kai fadar shugaban Chadi inda fadar shugaban ƙasar ta kira lamarin da "yunƙurin kawo hargitsi".

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet