Sport
Dollar
38,0166
0.27 %Euro
41,7417
-0.72 %Gram Gold
3.717,8900
-2.08 %Quarter Gold
6.293,2300
-0.18 %Silver
36,6500
-5.68 %Masu aikin ceto sun ceto wata mata mai shekaru 63 daga ɓaraguzan ginin da ke babban birnin Myanmar a ranar Talata, sai dai fatan samun ƙarin wasu da suka tsira daga mummunar girgizar kasar na ƙara dusashewa saboda matsalar ayyukan jinƙai.
Adadin waɗanda suka mutu sakamakon mummunar girgizar kasa mai karfin maki 7.7 da ta afku a Myanmar ya zarce 2,700, kana dubbai sun jikkata, kamar yadda Kafafen watsa labaran ƙasar suka ruwaito a ranar Talata.
Shugaban gwamnatin mulkin sojan Myanmar, Babban Janar, Min Aung Hlaing, ya shaida wa wani taron tattaunawa a babban birnin kasar, Naypyitaw cewa, a halin yanzu an samu gawawwakin mutane 2,719, yayin da wasu 4,521 suka jikkata, kana wasu 441 kuma ba a gansu ba.
Ana sa ran adadin zai ƙaru, la’akari da cewa har yanzu ba a iya kai wa ga wasu yankunan da girgizar kasar ta ranar Juma'a ta shafa ba domin aikin ceton jama’a.
Masu ceto sun ceto wata mata mai shekaru 63 daga ɓaraguzan ginin da ke babban birnin Myanmar a ranar Talata, sai dai fatan da ake da shi na samun karin wasu da suka tsira daga mummunar girgizar kasar na ƙara dusashewa, saboda taɓarɓarewar ayyukan jinƙai da ake fama da shi sakamakon yaƙin basasar ƙasar.
Hukumar kashe gobara a Naypyitaw ta ce an samu nasarar ciro matar daga ɓaraguzan ginin sa’o’i 91 bayan da ginin da ya ruguje ya binne ta sakamakon girgizar ƙasa mai karfin maki 7.7 da ta afku a ranar Juma’a.
Masana sun ce yiwuwar samun ƙarin wadanda suka tsira ya ragu bayan shafe sa'o'i 72.
Girgizar ƙasar ta afku ne a kusa da Mandalay, birni na biyu mafi girma a ƙasar.
Akwai yiwuwar alƙaluman za su ƙaru, duba da yadda girgizar ƙasar ta afka wa kusan dukka yankunan ƙasar, lamarin da ya haifar da katsewar wutar lantarki da hanyoyin sadarwa a wurare da dama, tare lalata hanyoyi da gadoji, lamarin da ya sa ba a iya tantance yawan ɓarnar da iftila’in ya haifar ba.
Comments
No comments Yet
Comment