Sport
Dollar
38,0382
0.25 %Euro
42,2521
0.14 %Gram Gold
3.807,7200
0.29 %Quarter Gold
6.304,8300
0 %Silver
39,0200
0.43 %Albanese, Wakiliya ta Musamman ta MDD a Yankin Falasɗinu da aka mamaye, ta ƙi yin ko gezau a yayin da ake yunƙurin kawo ƙarshen aikinta.
Francesca Albanese, Wakiliya ta Musamman ta MDD a Yankin Falasɗinu da aka mamaye, tana fuskantar matsin lamba daga ƙungiyoyin da ke goyon bayan Isra’ila da ‘yan siyasa da ke neman a kawo ƙarshen aikinta, kamar yadda jaridar The New Arab ta ruwaito.
A wannan makon ne wa’adinta na shekaru uku zai zo ƙarshen, kuma Majalisar Kare Hakkin Ɗan’adam ta MDD (UNHRC) za ta kaɗa ƙuri’a kan sabunra wa’adinta ranar 4 ga watan Afrilu.
Ƙasashe da dama sun nuna rashin goyon bayan sabunta wa’adinta saboda caccakar da take yi wa Isra’ila.
Albanese ta daɗe tana sukar Isra’ila game da abin da ta bayyana kisan ƙare-dangi da take yi wa Falasɗinawa.
Wani ɗan majalisar dokokin Birtaniya na jam’iiyyar Labour MP David Taylor, shi ne a kan gaba wajen sukar Albanese, inda ya zarge da goyon bayan harin da Hamas ta kai wa Isra’ila ranar 7 ga watan Oktoban 2023 sannan take ayyana Isra’ila a matayin ‘yar mamaya da "kama-wuri-zaua" a wata hira da ya yi da jaridar The Jewish Chronicle.
Ƙungiyoyin da ke goyon bayan Isra’ila, ciki har da UN Watch, suna ka gaba wajen sukarta.
UN Watch ta wallafa wani rahoto mai shafi 60 inda ta zargi Albanese da ƙyamar Yahudawa da “ta’addanci” a aikin da take yi wa MDD. Kazalika ƙungiyar ta yi kira ga UNHRC da ka da ta sabunta wa’adinta.
Comments
No comments Yet
Comment