Dollar

38,2757

0.03 %

Euro

43,5289

-0.4 %

Gram Gold

4.046,0600

-2.76 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Nijeriya dai tana fuskantar ƙalubale na tsaro a cikin gida, kuma kwanan nan ne wani bidiyo da ya nuna yadda wasu ‘yan China da ke raba wa wasu ‘yan sandan kwantar da tarzomar ƙasar kuɗi ya janyo kakkausar suka a shafukan sada zumunta a ƙasar.

Za a yi wa rundunar ‘yan sandan kwantar da tarzoma ta Nijeriya 'Mopol' garambawul

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta yi shelar sake tsara yadda ‘yan sandan kwantar da tarzomar ƙasar (mopol) ke gudanar da ayyukansu domin tunkarar matsalolin tsaro na cikin gida.

Sufeto Janar na ‘yan sandan ƙasar, Olukayode Adeolu Egbetokun, ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a wata ganawar da ya yi da kwamandodin ‘yan sandan kwantar da tarzoman a hedkwatar ‘yan sandan ƙasar a Abuja.

Wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan ƙasar, Olumuyiwa Adejobi, ya fitar ta ambato shugaban ‘yan sandan Nijeriya yana jaddada buƙatar sake tsara aikin ‘yan sandan domin su iya tunkarar tarzoma da buƙatar gaggawa da kuma barazanar tashin hankali.

“Ya nuna damuwa game da yadda ake juya akalar jami’an ‘yan sandan kwantar da tarzoma zuwa ayyukan da ba su shafe su ba, ciki har da rakiya da kuma gadi ga ɗaiɗaikun mutane da kuma manyan mutane, lamarin da ke yi wa ingancin rundunar zagon ƙasa,” in ji sanarwar.

Domin kauce wa wannan matsalar, sufetor janar ɗin ya yi shelar wasu matakai ciki har da janye dukkan ‘yan sandan kwantar da tarzoma daga ayyukan da ba a da izinin yi ba da horaswa bayan wata uku-uku kan ɗa’a da aiki bisa ƙa’ida da kuma tabbatar da cewa wasu cikin jami’an na zaune cikin ɗamara suna jiran ko ta kwana a ko wane lokaci, in ji Adejobi.

Kazalika shugaban ‘yan sandan Nijeriyar ya ce idan jami’an ‘yan sandan kwantar da tarzoman suka aikata ba daidai ba, kwamandojinsu ne za a ɗora wa laifin.

Saboda haka, ya ɓukaci kwamandojin su yi jagoranci na gari da horaswa na lokaci zuwa lokaci da kuma sa ido ta yadda jami’ansu za su yi aiki da ɗa’a da martaba ‘yancin ɗan’adam da kuma inganci.

Nijeriya dai tana fuskantar ƙalubale na tsaro a cikin gida, kuma kwanan nan ne wani bidiyo da ya nuna yadda wasu ‘yan China da ke raba wa wasu ‘yan sandan kwantar da tarzomar ƙasar kuɗi ya janyo kakkausar suka a shafukan sada zumunta a ƙasar.  

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#