Sport
Dollar
38,1314
0.12 %Euro
43,6678
1.4 %Gram Gold
4.084,5100
3.27 %Quarter Gold
6.731,9300
3.38 %Silver
40,3700
1.95 %Onanuga ya ce Shugaba Tinubu bai bai wa kowa damar yi masa yaƙin neman zaɓe a ko wace kafar watsa labarai ba har sai lokacin da hukumar zaɓen Nijeriya (INEC) ta fitar da jadawalin zaɓen 2027.
Fadar shugaban Nijeriya ta nuna damuwa game da yadda wasu ke kafa allunan yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu na shekarar 2027 a faɗin ƙasar.
Wata sanarwa da mai bai wa Shugaba Tinubu shawara kan watsa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar ta ce duk da cewa Shugaba Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima suna maraba da karsashin magoya bayansu a faɗin ƙasar, shugabannin biyu ba sa goyon bayan soma yaƙin neman zaɓen da ya saɓa wa doka.
Sanarwar ta ce dokar zaɓen ƙasar ba ta amince da fara yaƙin neman zaɓe ba tun da ba a fitar da jadawalin zaɓe ba.
“A matsayinsu na shugabanni masu bin doka, Shugaba Tinubu da Mataimakin Shugaba Shettima ba sa goyon bayan duk wani mataki da zai iya yi wa ma’aikatunmu da kuma tsarin zaɓe zagon-ƙasa,” in ji sanarwar.
Onanuga ya ce Shugaba Tinubu bai bai wa kowa damar yi masa yaƙin neman zaɓe ba ta ko wace kafar watsa labarai har sai lokacin da hukumar zaɓe INEC ta fitar da jadawalin zaɓen 2027.
“Saboda haka, muna kira cikin gaggawa ga mutane da ƙungiyoyi da ke ɗaukar nauyin wannan yaƙin neman zaɓen 2027 kan alluna a faɗin ƙasar su daina nan-take. Shugaba Tinubu da mataimakinsa sun dage wajen aikin da suka tsara wa kansu na gina ƙasa da suke yi,” in ji sanarwar.
“Wannan dagewan a bayyane yake bisa ga yadda suka mayar da hankali kan farfaɗo da tattalin arziki da inganta ƙwarewar mutane da tallafa wa al’umma da kuma tsaron ƙasa,” in Onanuga.
A shekarar 2023 ne aka zaɓi Shugaba Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima a Nijeriya, kuma za su gama wa’adinsu na farko ne a shekarar 2027.
Comments
No comments Yet
Comment