Dollar

38,0489

0.04 %

Euro

43,2285

0.02 %

Gram Gold

3.945,3900

0.48 %

Quarter Gold

6.469,8500

0 %

Silver

39,4700

-0.27 %

Domin ka da a bar sauran jihohin a baya, shi ya sa mataimakin shugaban Nijeriya, Kashim Shettima ya halarci taron samar da abinci na Duniya a birnin Rome domin samo kuɗin faɗaɗa tsarin ga ƙarin jihohi, in ji ministan.

Ba mu hana Jihohin Arewa Maso Gabashin Nijeriya cibiyoyin sarrafa amfanin gona ba — Abubakar Kyari

Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta ce ba ta hana jihohin Arewa Maso Gabashin ƙasar samun cibiyoyi na musamman na sarrafa amfanin gona (SAPZ) ba, saɓanin koken da ‘yan majalisar tarayya daga yankin suka yi.

‘Yan majalisar tarayya daga yankin Arewa Maso Gabas sun yi ƙorafin cewa an nuna wa yankin wariya game da samar da cibiyoyin SAPZ ɗin ne bayan an ƙaddamar da mataki na farko na shirin samar da cibiyoyin na sarrafa amfanin gona a jihar Kaduna ranar 8 ga watan Afrilu.

Sanatoci da ‘yan majalisar wakilai daga jihohin Adamawa da Bauchi da Borno da Gombe da Taraba da kuma Yobe sun ce ba daidai ba ne a ce babu wata jiha daga Arewa Maso Gabashin ƙasar da ta samu wannan cibiya.

“Muna kira da a yi gaggawar saka yankin Arewa Maso Gabashi cikin waɗanda za su ci gajiyar cibiyoyi na musamman na sarrafa amfanin gona. Wannan ba wai domin yin adalci ba ne kawai, amma domin tabbatar da manufar wannan gwamnatin ta mayar da fannin noman Nijeriya fanni mai aiki da masana’antu da kuma samar da ayyuka masu ɗorewa a ƙasar,” in ji su.

Sai dai kuma Ministan Noman Nijeriya, Abubakar Kyari, ya ce ‘yan majalisar sun yi kuskure domin gwamnatin ba ta nuna wa jihohin yankin wariyar hana su cin gajiyar shirin ba.

 A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Abubakar Kyari ya ce jihohin Kaduna da Kano da Kwara da Oyo da Ogun da Imo da Cross River da kuma Birnin Tarayya Abuja su ne suka rubuta takardar neman cibiyoyin kuma suka cika sharuɗɗan ba da cibiyoyin tun lokacin da aka fara shirin a shekarar 2019.

Domin ka da a bar sauran jihohin a baya, shi ya sa mataimakin shugaban Nijeriya, Kashim Shettima ya halarci taron samar da abinci na Duniya a birnin Rome domin samo kuɗin faɗaɗa tsarin ga ƙarin jihohi, in ji ministan.

Ya ƙara da cewa a birnin Rome ɗin ne shugaban bankin raya tattalin arziƙin Afirka AfDB ya yi alƙawarin samar da dala biliyan ɗaya wa shirin domin a faɗaɗa shi.

Kazalika, ministan ya ce jihohi 27 ne suka nemi a saka su cikin mataki na biyu na shirin, sai dai kuma jihohi 10 ne suka cika sharruɗan shiga cikin shirin kuma jihohin Borno da Gombe da Bauchi daga arewa maso gabashin Nijeriya na cikin jihohi goman da suka samu shiga mataki na biyu na shirin.

Ministan ya ce yana fatan cewa sauran jihohin ƙasar da ba su samu shiga shirin ba za su yi ababen da suka dace domin cika sharruɗan shiga shirin domin haɓaka fannin noman a jihohin da ma Nijeriya gabaɗaya.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#